Cristiano Ronaldo ya zama ɗan wasan ƙwallon ƙafa na farko da ya zama biloniya a tarihin wasanni, a cewar kamfanin bayanan kuɗi da labarai, na Bloomberg.
Bloomberg Billionaires Index, wanda ke bibiyar jerin mutanen da suka fi kuɗi a duniya bisa dukiyarsu, ya bayyana cewa an ƙididdige dukiyar ɗan wasan mai shekara 40 na ƙasar Portugal kuma ɗan wasan Al-Nassr ne a karon farko.
Ƙididdigar ta haɗa da abin da ya samu daga aikinsa, jarinsa, da kuma yarjejeniyoyin tallace-tallace. Rahoton ya ce dukiyar Ronaldo ta kai dala biliyan 1.4 (£1.04bn).
An bayyana cewa ya samu fiye da dala miliyan 550 (£410m) daga albashi tsakanin shekarar 2002 da 2023, tare da ƙarin kuɗaɗen da yake samu daga yarjejeniyoyin tallace-tallace da kamfanoni, ciki har da yarjejeniyar shekara goma da kamfanin Nike wacce take kai kusan dala miliyan 18 (£13.4m) a shekara.
Lokacin da Ronaldo ya koma kungiyar Al-Nassr a gasar ƙwallon ƙafa ta Saudiyya a shekarar 2022, ya zama ɗan wasan da yake samun albashi mafi tsada a tarihin ƙwallon ƙafa, da albashin shekara mai darajar fam miliyan 177 (£177m).
Yarjejeniyarsa ta farko za ta ƙare ne a watan Yunin 2025, amma ya sake sanya hannu kan wata yarjejeniya ta shekaru biyu wacce rahotanni suka ce ta kai fiye da dala miliyan 400 (£298m) wanda zai sa ya ci gaba da wasa har bayan ya kai shekara 42.
A ɓangare guda, ɗan wasan Argentina kuma tauraron Inter Miami, Lionel Messi, wanda ya yi gasa da Ronaldo tsawon shekaru a ƙasar Sifaniya, ya tara fiye da dala miliyan 600 (£447m) daga albashinsa kafin haraji, a cewar Bloomberg.
Wannan ya haɗa da albashin shekara mai darajar dala miliyan 20 (£15m) tun daga shekarar 2023, wanda ke daidai da kusan kashi 10% na abin da Ronaldo ke samu a wannan lokaci.
Bayan ya yi ritaya, ana sa ran cewa Messi zai samu rabo na hannun jari a ƙungiyar Inter Miami