Shugaban Gidauniyar bayar da tallafin ilmi a manyan makarantun gaba da Sakandare "TETFund" ya bayar da tabbaci cigaba da inganta Aiyyukan ilimi a faɗin Kasar. Shugaban Kwamitin Amintattu (BOT) na TETFund kuma Tsohon Gwamnan Jihar Katsina Rt Hon Aminu Bello Masari, CFR ne ya bayyana haka. A ranar Laraba 09/101/2025, a cikin jawabinsa na maraba, a wajen zauren tattaunawa da al'umma Wanda ya gudana a dakin taro na A-Class dake babban birnin Abuja.
Rt Hon Aminu Bello Masari ya ce TETFund za ta cimma wannan manufa ne ta hanyar karfafa lura da yadda ake amfani da kudin hukumar, da inganta nazari da binciken masana cikin harkikin aikin gona da lafiya da kimiyya da fasahar zamani.
Har ila yau za a ƙarfafa alaƙa da haɗin gwiwa da manyan masana'antu da ƙungiyoyin samar da cigaba na ƙasa da ƙasa. Shugaban Ya bayyana cewa" samar da nagartaccen ilmi na bukatar gudunmuwar al'umma, musamman masana da kamfanoni da kungiyoyin fararen hula (CSOs) da sauran al'umma masu kishin kasa.
Hakan ne ya sa aka hadu a wannan taro don a kara samun shawarwari da goyon bayan jama'a din samun cinma manufofin TRTFund a kasar nan. Bugu da ƙari, ya yi jawabi cikakke kan ƙoƙarin da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ke yi da bayar da kyakkyawan yanayi da dinbin kuɗi don tabbatar da cewa ɗalibai 'yan Najeriya sun samu ingantaccen ilimi a manyan makarantun ƙasar nan.
Daga karshe ya bayar da misalai na mayan ayyuka gine gine da horar da Malamai a ma'aikata tare da samar ingantattun kayayyakin horarwa, a dakunan bincike da gwaje gwaje. Ya kuma tabbatar da ƙoƙarin inganta bincike a sassan samar da makamashi na zamani (Renewable Energy) da kimiyya da fasahar zamani.
A nasa jawabin, Sakataren Zartarwa na TETFund, Arc. Sonny S.T. Echono, ya yaba da irin goyon bayan da Shugaba Tinubu ke baiwa Asusun, tare da tabbatar da cewa za a ƙaddamar da ƙarin ayyuka da suka haɗa da samar da wutar lantarki da ɗakunan kwana ga ɗalibai a jami’o’i da kwalejoji a duk faɗin ƙasa.
A cewar Echono, “Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ɗorewar TETFund. Za mu ci gaba da inganta yanayin koyarwa da karatu tare da tabbatar da cewa dukkan cibiyoyin ilimi sun amfana da ayyukan Asusun.”
Shi ma a nashi jawabin, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da ilimi na manyan makarantu, Sanata Muntari Dandutse, ya tabbatar da cewa Majalisar ƙarƙashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio za ta ci gaba da goyon bayan TETFund domin dorewar ci gaba.
Ita ma Shugabar Kwamitin Majalisar Wakilai kan TETFund da Sauran Ayyuka, Hajiya Princess Miriam Onuoha, ta gode wa Shugaba Tinubu bisa cire sashen da ke neman kawo ƙarshen TETFund a sabon kudirin haraji, tana mai cewa hakan alama ce ta cikakken goyon bayan gwamnati ga ci gaban ilimi a Najeriya.
Tun da farko, Sakatare na Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, wanda Mr. Olusegun Adekunle, Babban Sakataren Dindindin a ofishinsa ya wakilta, ya yaba da irin rawar da TETFund ke takawa wajen ci gaban ilimi tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da bayar da goyon baya.
Haka kuma, wakilin Ministan yaɗa labarai wanda Shugaban Hukumar FRCN ya wakilta ya tabbatar da cewa ma’aikatar sa za ta ci gaba da haɗin gwiwa da TETFund wajen yaɗa bayanai da tallata nasarorin Asusun a faɗin ƙasar baki ɗaya. Taron ya tattatara manyan jami’an gwamnati, shugabannin jami’o’i, ’yan majalisa, masana da sauran masu ruwa da tsaki, inda aka jaddada ƙudurin haɗin kai wajen ƙara inganta tsarin ilimin manyan makarantu a Najeriya.
