Cutar Typhoid Da Yadda Ake Kamuwa Da Ita

NENE TYPHOID?

Kamar yadda aka bayyana a shafin "Lafiya Uwar Jiki" na Facebook, Typhoid cuta ce da ke kama hanji da jini, wadda ke haddasa ƙwayar cuta mai suna Salmonella typhi. Wannan ƙwayar tana rayuwa a cikin jikin ɗan'Adam, kuma tana yaɗuwa ta hanyar rashin tsafta  musamman ta abinci da ruwa masu ƙazanta. Cutar na yaɗuwa sosai a yankunan da ba a samun ingantaccen tsafta da ruwa mai kyau, musamman lokacin damina ko ambaliya.

Typhoid

ALAMOMIN CIWON TYPHOID:

Alamomin na iya bayyana a hankali bayan kwana 6 zuwa 30 da kamuwa da cutar:

.Zazzaɓi mai zafi

.Ciwon kai mai zafi

.Ciwon ciki

.Rashin ci ko rage jin yunwa

.Gajiya sosai da ciwon jiki

.Amai ko jin tashin zuciya

.Yana iya sa gudawa ko kuma rashin yin bayan gida (constipation)

Idan ba a magance cutar da wuri ba, tana iya haddasa tsagewar hanji (intestinal perforation), zubar da jini, ko ma mutuwa.

YADDA TYPHOID KE YAƊUWA (Mode of Transmission):

Cutar na yaɗuwa ta hanyar:

1. Shan ruwan mai datti ko wanda ƙwayar cutar ta gauraya da shi.

2. Cin abinci marar tsafta .

3. Mutum zai iya ɗaukar cutar idan bai wanke hannu bayan zuwa bayan gida ba.

4. Rashin wanke ɗanyen kayan lambu da kyau.

5. ko ta hanyar ƙuda.

YADDA AKE GANO TYPHOID TA HANYAR GWAJI (Diagnosis):

Ta hanyar gwaji kawai ake gane typhoid, ba a taƙaita ga alamu kaɗai ba.

1. Widal Test: Gwajin jini da ke nuna alamar cutar.

2. Blood Culture: Mafi aminci  yana gano ƙwayar cutar kai tsaye daga jini.

3. Stool & Urine Test: Gwajin bayan gida ko fitsari don gano kwayar cuta

HANYOYIN KARE KAI DAGA TYPHOID (Prevention):

Tsafta ita ce hanya mafi muhimmanci.

A sha ruwa mai tsafta wanda aka dafa ko aka tace.

A dafa abinci da kyau.

A wanke hannu da sabulu bayan zuwa bayan gida.

A wanke hannu da sabulu kafin da kuma bayan cin abinci.

A guji sayen abinci daga wuraren da ba a tabbatar da tsafta ba (kamar kan titi).

A guji amfani da ruwa marar tsafta.

SHAWARWARI DANGANE DA CIWON TYPHOID (Typhoid): 

 Ana bada shawarar zuwa asibiti don a tabbatar da cutar kafin a fara magani.

A sha ruwa sosai don hana bushewar jiki.

Kada a tsaya ana shan magani a gida ba tare da tabbatar da cutar ba, hakan zai iya haddasa juriya ga magani wato (drug resistance).

Typhoid cuta ce mai hatsari amma ana iya guje mata ta hanyar kulawa da tsafta. Idan kana da alamomin typhoid, kar ka yi jinkiri ka ziyarci asibiti.

Post a Comment

Previous Post Next Post