An ce ɗalibin ya yi tsokaci mai sosa rai kan manufofin gwamnati a kafar sada zumunta.
Jami’an tsaro a Najeriya sun kama wani ɗalibi mai suna Abubakar Isa Mokwa, ɗalibi a Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU), Lapai, bisa zargin ya yi suka ga Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Muhammed Umaru Bago, a shafukan sada zumunta.
Rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana cewa ‘yan sanda sun damƙe ɗalibin ne bayan da wasu jami’ai suka kai rahoton cewa ya wallafa rubutun da ke sukar manufofin gwamnati, wanda suka bayyana da cewa “yana iya tayar da fitina”.
Wata majiyar jami’ar ta bayyana cewa an kai ɗalibin ofishin ‘yan sanda a Minna domin ci gaba da bincike, yayin da wasu ɗalibai da ƙungiyoyi ke neman a sake shi, suna cewa ya yi amfani ne da ‘yancin faɗar albarkacin baki.
Hukumomi dai har yanzu ba su bayyana taƙamaiman abin da ɗalibin ya faɗa ba, sai dai masana harkokin gwamnati sun ja hankalin jami’an tsaro da su tabbatar da cewa ‘yancin ɗalibai na yin magana ba ya zama dalilin tsangwama ko kama su, musamman idan suna magana cikin natsuwa da hujja.