Gwamnan Jihar Katsina Ya Tsige Kwamishinoni Biyu, Ya Kirkiri Sabuwar Ma’aikata

 Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da yin sauye-sauye a majalisar zartarwa ta jiha, wanda ya haɗa da canjin mukaman kwamishinoni, kirkirar sabuwar ma’aikata, tare da nada sabbin masu ba da shawara guda biyu.

Sabbin kwamishinoni

Wannan sauyi da zai fara aiki nan take, yana da nufin ƙarfafa tsarin aiki da inganta samar da ayyuka ga al’umma a fannoni daban-daban na gwamnati.

A cewar sanarwar, gwamnan ya tsige kwamishinoni biyu, yayin da wasu kuma aka maye gurbinsu ko aka sauya musu ma’aikata.

A sabon tsarin, Hon. Adnan Nahabu ya zama Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi, Sana’o’i da Horo na Fasaha, yayin da Farfesa Ahmad Muhammad Bakori, wanda a baya ke jagorantar Ma’aikatar Harkokin Noma da Kiwo, yanzu zai shugabanci sabuwar Ma’aikatar Harkokin Kiwo da aka kirkira.

Hon. Aliyu Lawal Zakari ya koma daga Ma’aikatar Wasanni da Harkokin Matasa zuwa Ma’aikatar Noma, yayin da Hajiya Zainab Musa Musawa ta bar Ma’aikatar Ilimi na Firamare da Sakandare zuwa ta Harkoki na Musamman.

Haka zalika, Hon. Yusuf Suleiman Jibia ya zama Kwamishinan Ilimi na Firamare da Sakandare, yayin da Injiniya Surajo Yazid Abukur ya karɓi ragamar Ma’aikatar Wasanni da Harkokin Matasa.

Tsohuwar Darakta Janar ta Hukumar Inganta Harkokin Kasuwanci ta Jiha, Hajiya Aisha Aminu, yanzu ita ce Kwamishinar Harkokin Mata.

Bugu da ƙari, Gwamna Radda ya nada Hajiya Hadiza Abubakar Yar’adua a matsayin Mai Ba da Shawara ta Musamman kan Abinci mai Gina Jiki da Walwala, tare da Isa Muhammad Musa a matsayin Mai Ba da Shawara ta Musamman kan Al’adun Gargajiya.

Gwamna Raɗɗa ya jaddada kira ga sabbin shugabanni da su kasance masu jajircewa, gaskiya da kishin kasa wajen gudanar da ayyukansu, domin cika manufar gwamnatinsa ta “Gina Makoma” (Building Your Future Agenda).

Ya kuma bayyana cewa wannan sauyin zai taimaka wajen inganta hadin kai, kwarewa a fannoni daban-daban, tare da aiwatar da shirye-shiryen gwamnati a bangaren ilimi, noma, kiwon lafiya, matasa, mata da walwalar al’umma.

Post a Comment

Previous Post Next Post