Dalilan Da Ke Sa A Ji Kasala Bayan An Tashi Barci

 Mutane da dama na fuskantar matsala a yayin da suka zo barci ko kuma suke yin barci. Wasu kuma ba sa samun matsala har sai idan sun tashi barcin. Mutum kan wayi gari da matsananciyar gajiya a yayin da ya tashi barci. Idan kana fuskantar irin wannan matsalar, ga wasu daga cikin dalilan da ke janyo hakan:

Hoton Mai Barci Cikin Gajiya

1. Rashin Yin Barci Mai Zurfi (Deep Sleep Deprivation) Idan kana tashi sau da dama a cikin dare, jikinka ba ya shiga "deep stage" na bacci wanda a nan ake gyaran jiki da kwakwalwa. hakan na iya haddasa matsananciyar gajiya bayan an tashi bacci, kuma yana hana "hormones" kamar "melatonin" da "growth hormone aiki yadda ya kamata. Sai ka ji ka tashi ba kuzari.

2. Cin Abinci Mai Nauyi Kafin Bacci

Cin abinci mai nauyi da kayan zaƙi kafin barci yana hana cikinka hutawa. Yana sa "acid reflux" da kuma rashin samun natsuwar bacci. Ka rage cin abinci aƙalla awanni biyu kafin bacci.

3. Stress da Damuwa (Mental Stress)

 Damuwa tana rage iskar da ƙwaƙwalwa ke samu yayin bacci, hakan na iya sa ka farka da safe kamar wanda bai kwanta ba. Ka rika yin addu’a domin ka yi "clearing" damuwarka kafin ka kwanta.

4. Shan "Caffeine" Kusa da Lokacin Bacci: Coffee, energy drink, ko soft drink kafin bacci suna hana deep sleep. Ka Guji caffeine bayan 4:00pm

5. Karancin Jini Ko "Iron Deficiency"

Idan jininka ya yi ƙasa, jikinka ba ya samun isasshen "oxygen", hakan ke sa jin gajiya duk safiya. Ka duba jinin ka (PCV, Hb) sannan ka riƙa cin abincin da ke ɗauke da iron kamar zogale, kwai da kifi.

6. Rashin Ruwa a Jiki (Dehydration): Idan ba ka shan ruwa sosai, jini baya gudana yadda ya kamata yayin bacci, hakan zai janyo ciwon kai, gajiya, da rashin kuzari da safe.

7.Matsalar Hormones (Thyroid ko Cortisol Imbalance)

Mutanen da ke da "thyroid" da "cortisol disorder" suna yin bacci amma suna tashi gajiye. Ka duba thyroid function test idan kana fama da wannan akai-akai.

Bacci lafiya ne, kuma hutu ne ga ƙwaƙwalwa da gangar jikin ɗan'Adam. Mutum na iya ziyartar likita domin gudanar da gwajegwaje idan yana fuskantar matsala a yayin bacci ko kuma bayan farkawa daga bacci.

Post a Comment

Previous Post Next Post