Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto Ta Yi Fice A Wasannin Zakarun NUGA Zone D

Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto (UDUS), ta samu gagarumar nasara a wasannin zakarun Nigeria University Games Association (NUGA) Zone D da aka gudanar a Sokoto, inda ta samu damar zuwa gasar NUGA ta ƙasa.

Shugaban masu horas da ‘yan wasa na jami’ar, Jacob Olubayo Atunwa, ya bayyana cewa UDUS ta samu gurbi a fannoni da dama ciki har da ƙwallon kafa, ƙwallon hannu, ƙwallon raga ta mata, dambe, wasannin motsa jiki (athletics), iyo, da kuma cricket.

A wasan ƙarshe na ƙwallon ƙafa da aka buga a filin wasa na Giginya Memorial Stadium, tawagar UDUS ta doke Jami’ar Jihar Sokoto (SSU) da ci 2–0, inda Jeremiah Samuel da Danjuma Bawa suka zura ƙwallo daya-daya.

Da yake bayyana shirye-shiryen da jami’ar ke yi don gasar NUGA mai zuwa, Kocin Atunwa ya ce:

“Yanzu da an kammala wasan zakarun, za mu yi amfani da lokacin da ya rage wajen ƙara ƙaimi a horo domin babban gasar. Ina godiya ga shugabancin jami’ar bisa samar da yanayi mai kyau ga harkokin wasanni, da kuma taya ‘yan wasanmu murna da za su wakilci UDUS a gasar NUGA da za a gudanar a Jos.”

Jami’ar UDUS za ta halarci gasar NUGA da za a gudanar a Jami’ar Jos daga ranar 5 zuwa 16 ga Nuwamba, tare da tawaga mai ƙarfi da ta ƙunshi ‘yan wasa 54 da jami’ai hudu.

Post a Comment

Previous Post Next Post