Masu Bincike Uku Za Su Karbi Kyautar Nobel Na Tattalin Arziki Saboda Gudummawarsu Kan Ci Gaban Da Fasaha Ke Haifarwa

 

Masu Ƙirƙira

An bai wa masana uku kyautar Nobel ta tattalin arziki a bana saboda binciken su kan yadda ƙirƙire-ƙirƙire da sabbin fasahohi ke ƙarfafa ci gaban tattalin arziki. Hukumar Nobel ta bayyana cewa binciken nasu ya taimaka wajen fahimtar yadda ƙasashe ke samun ci gaba ta hanyar saka jari a fannin ilimi, fasaha da ƙirƙira.

Masu binciken sun nuna cewa ƙarfafa kamfanoni, da masana su riƙa ƙirƙirar sabbin abubuwa na iya ƙara samar da ayyukan yi da haɓaka tattalin arziki. Hakan, in ji kwamitin Nobel, yana da muhimmanci musamman a wannan zamani da tattalin arzikin duniya ke fuskantar ƙalubale daga sauyin yanayi da raguwar albarkatu.

Post a Comment

Previous Post Next Post