Dalilin Da Yasa Jam’iyyar PDP Ta Ki Sayar Wa Sule Lamido Da Fom Din Takara

 Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma babban jigon jam’iyyar PDP, Sule Lamido, ya zargi shugabancin jam’iyyar da hana shi sayen fom ɗin takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar, kafin taron gangamin da za a gudanar nan gaba.

Sule Lamido

Lamido ya isa hedikwatar PDP (Wadata Plaza) da ke Abuja domin sayen fom ɗin, amma a cewarsa, Ofishin sakataren shirye-shirye na jam’iyyar wanda ke da alhakin sayar da fom ɗin, ya kasance a rufe, kuma jami’an da ke wurin sun ce ba su da masaniya a kan inda ake rarraba fom ɗin.

Ya ce an miƙa alhakin sayar da fom ɗin ga kwamitin shirya taron ƙasa (NCOC) wanda gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ke jagoranta.

Lamido ya nuna bacin ransa inda ya ce: “Idan ba su ba ni fom ɗin ba, zan kai ƙara kotu. Shi kenan.”

Ya bayyana wannan lamari a matsayin wata maƙarƙashiya da nufin hana shi shiga takara da kuma murƙushe ra’ayoyinsa a cikin jam’iyyar.

A halin da ake ciki, wasu daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar sun nemi a kwantar da hankali, inda suka shawarci Lamido da sauran masu neman takara da su bi hanyoyin cikin gida na jam’iyyar wajen warware sabani maimakon kai kara kotu.

Post a Comment

Previous Post Next Post