Sanusi: Jonathan Ya Dakatar Da Cire Tallafin Fetur Saboda Tsoron Boko Haram


Sunusi Lamido

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya dakatar da shirin cire tallafin fetur a shekarar 2012 saboda tsoron cewa ’yan ta’addan Boko Haram za su iya kai hari ga masu zanga-zangar da ke adawa da matakin.

Goodluck

A wancan lokacin, an gudanar da zanga-zanga ta ƙasa baki ɗaya wadda ta ɗauki kusan makonni biyu, ta kuma durƙusar da harkokin kasuwanci da sufuri a faɗin ƙasar.

A cewar rahoton da TheCable ta wallafa, Sanusi, wanda shi ne Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) a wancan lokaci, ya bayyana cewa an yi kuskuren fahimtar manufar cire tallafin fetur da kuma yadda gwamnati ta gudanar da shi a lokacin.

Ya bayyana hakan ne yayin taron Oxford Global Think Tank Leadership Conference da aka gudanar a ranar Talata, mai taken “Better Leader for a Better Nigeria.”

Sanusi ya ce tsarin tallafin fetur a Najeriya a lokacin ya kasance tamkar “naked hedge”, wato gwamnati na ɗaukar nauyin tabbatar da farashin fetur bai tashi ba, duk da sauyin farashin man duniya ko kuma ribar bashin da ake ɗauka.

Ya bayyana cewa hakan ya sa gwamnati ta shiga cikin bashi mai yawa, inda ake amfani da kuɗaden da ake samu daga albarkatun ƙasa wajen biyan tallafi, sannan daga baya aka fara ɗaukar bashi domin biyan tallafin, har ma da ribar bashin da aka ɗauka don tallafin kansa. “Idan ka kalli tsarin, duk wannan nauyi ne da gwamnati ta ɗauka kamar tana da aljihun da ba ya ƙarewa,” in ji Sarkin Sanusi.

“Mun fara daga amfani da kuɗin shiga wajen biyan tallafi, zuwa ɗaukar bashi don biyan tallafi, sannan daga baya zuwa ɗaukar bashi don biyan ribar bashin tallafin. Wannan tsarin ne da ya jefa ƙasar cikin halin rashin kuɗi (bankruptcy).”

Sanusi ya ƙara da cewa, wannan misali yana nuna yadda rashin tsari a cikin manufofin gwamnati ke iya haifar da matsalar tattalin arziki da dogon lokaci na durƙushewar ƙasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post