Dan Majalisa Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC A Zamfara

Siyasar Zamfara na ƙara ɗaukar sabon salo, bayan da ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Maradun II a Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon. Maharazu Salisu Faru, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

A wata wasiƙa da ya aike wa da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta hannun Sakataren Majalisar, Faru ya bayyana cewa ya bar PDP ne sakamakon, a cewarsa, “rashin ingantaccen shugabanci” da ke damun jam’iyyar, musamman a matakin ƙasa da kuma na jiha.

Ya ce bayan yin doguwar shawara da jama’ar mazaɓarsa, sun amince da matakinsa na komawa jam’iyyar APC domin su kasance tare da gwamnatin da ke kan mulki a jihar.

Faru, wanda ke shugabantar Kwamitin Dindindin na Majalisar kan Shari’a da Hukumomi, ya ce sauya shekar tasa ta fara aiki daga ranar 28 Oktoba, 2025.

Sauya shekar tasa na daga cikin jerin ‘yan majalisar da suka koma APC a ‘yan kwanakin nan, lamarin da ake ganin zai ƙara ƙarfafa rinjayen jam’iyyar mai mulki a cikin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara.

Post a Comment

Previous Post Next Post