Dangantakar Sarki Faisal Na Saudiyya Da Sheikh Ibrahim Inyass

Sarki Faisal na Saudiyya da Sheikh Ibrahim Inyass sun ƙulla alaƙa ta musamman wacce ta samo asali daga ganawarsu ta farko, inda Shehin Malamin a lokacin ya yi wa Faisal addu'ar Allah ya ba shi mulkin Saudiyya. A lokacin da Faisal ya zama sarki, su biyun sun zama abokan ƙut da ƙut da kuma haɗa ƙarfi don kafa ƙungiyar ƙasashen musulmi ta duniya.

GANAWA A MAKKA (1963)

Yarima Faisal, wanda a lokacin shi ne ɗan Sarki Abdul Aziz na uku, kuma yana neman gadon sarauta, ya hadu da Sheikh Ibrahim Inyass a lokacin aikin Hajji. Ya roki Shehin Malamin da ya yi masa addu’a ya zama Sarki na gaba, duk da bambancin akida da ke tsakanin Faisal na zamansa bawahabiye da Sheikh Ibrahim Inyass a matsayin sa na Sufi (Tijjaniyya). Daga baya an nada Faisal sarautar Saudiyya duk da cewa akwai yayyensa guda biyu. Bayan nadin sarautar Faisal ya bai wa Sheikh Ibrahim Inyass damar shiga Saudiyya duk lokacin da ya ga dama ba tare da Biza ba.

KYAUTAR KUDI (1965)

A wani aikin Hajji a 1965, Sarki Faisal ya ba wa Sheikh Ibrahim cakin kudi, don ya rubuta adadin kudin daya ga dama. Sai Sheikh Ibrahim Inyass ya nuna rashin jin dadinsa da hakan, sai kawai ya rubuta adadin kudin siyen littafin hadisi na Riyal 35, wanda hakan ya bai wa Sarki mamaki tare da kara masa mutunci.

Sarki Faisal Da Sheikh Ibrahim Inyass

HADIN KAN MUSULMI A KASASHEN DUNIYA 

Dangantakar su ta wuce mu'amala tsakanin mutum da mutum. Sheikh Ibrahim Inyass ya zama Mataimakin Shugaban Kungiyar Kasashen Musulmi ta Duniya, inda Sarki Faisal ya zama Shugaban Kungiyar. Sarkin ya na mutunta ra'ayin Sheikh Ibrahim a matsayin mai ba da fatawa mai inganci (ra'ayin shari'a na Musulunci).

ZIYARAR SARKI FAISAL A SENEGAL A SHEKARAR 1973

A wani mataki da ba a taɓa ganin irinsa ba, Sarki Faisal ya kai ziyarar ba-zata ga Sheikh Ibrahim Inyass a birnin Kaolack a kasar Senegal a watan Maris na 1973. An ce shi ne Sarkin Saudiyya na farko kuma daya tilo da ya kai ziyara Senegal. 

An ruwaito cewa Sarki Faisal ya ce, "Muna da raudar Annabi Muhammad (SAW) a Madina, amma soyayyar Manzon Allah (SAW) ta na Madina Baye!" cibiyar ruhin Sheikh Ibrahim Inyass.

Post a Comment

Previous Post Next Post