Ƙungiyar Concerned Ulama of Sunnah ta shigar da ƙorafi ga hukumomin da suka dace tana zargin wasu malamai da yin ɓatanci, ɓata suna, da kuma tayar da fitina a tsakanin al’umma ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta.
A cewar kungiyar, wasu daga cikin malamai sun fara yin amfani da Facebook, YouTube, da WhatsApp wajen yada kalamai masu tunzura jama’a da kuma kawo rarrabuwar kai tsakanin mabiya Sunnah.
Wani daga cikin shuwagabannin kungiyar ya bayyana cewa: “Mun damu matuƙa da irin yadda ake amfani da sunan addini wajen cin mutuncin juna, musamman tsakanin malamai da ake ganin su ne ginshiƙin al’umma. Wannan abin takaici ne, domin yana iya janyo fitina da lalata amincin al’umma.”
Ƙungiyar ta buƙaci hukumomin tsaro da na addini su dauki matakin gaggawa domin hana irin wadannan abubuwan ci gaba, tare da tabbatar da cewa addinin Musulunci ya ci gaba da zama hanyar zaman lafiya da fahimtar juna.
An bayyana cewa kungiyar ta gabatar da cikakken rahoton ƙorafin ga hukumomi domin bincike da daukar mataki.
Hoton da ya fito tare da rahoton ya nuna Young Imam da Nasiru Shuaibu Babbar Harka, wadanda ake alakanta da lamarin a kafafen sada zumunta.