Sunaye Da Bayanan Hafsoshin Sojojin Nijeriya 16 Da Aka Tsare Saboda Zargin Makircin Juyin Mulki

Sunaye da bayanai na hafsoshin sojojin Najeriya guda 16 da aka tsare saboda zargin makircin juyin mulki. Bayanan hafsoshin da ake tsare saboda zargin makircin juyin mulki

Sojoji 16 Da Ake Zargi Da Juyin Mulki

1. Birgediya Janar Musa Abubakar Sadiq

   An haife shi a ranar 3 ga Janairu,1974. Birgediya Janar ne mai lamba N/10321. Ya samu horo a matsayin NDA cadet daga ranar 14 ga Agusta, 1992 zuwa 20 ga Satumba, 1997. Ana zarginsa a matsayin shugaban makircin. Memba ne na Regular Course 44.Janar Sadiq, ɗan asalin jahar Nasarawa ne, ya yi girma a cikin mukamai, ya zama Kanal a shekarar 2015, sannan ya zama Birgediya Janar bayan shekaru hudu. Yana cikin rukunin sojan kaki.

Ba wannan karo ba ne na farko da Janar Sadiq ya fito a cikin labarai saboda zargin manyan laifuffuka. A watan Oktoba na 2024, an ruwaito cewa an tsare shi saboda "zargin satar kayayyakin taimako na shinkafa, da sayar da kayan aikin soja, ciki har da janareto da motocin aiki zuwa wuraren da ake jujjuyawa." Daga cikin sauran mukamai, hafsin ya yi aiki a matsayin Kwamandan Brigade na 3 a Kano da kuma Kwamandan Garrison na Sashen Soja na 81 a Lagos.

2. Kanal M.A. Ma’aji

   Kanal Ma’aji mai lamba N/10668.An haife shi a ranar 1 ga Maris, 1976. Dan kabilar Nupe ne daga jahar Niger. Ya fara horo a ranar 18 ga Agusta, 1995, ya kammala a ranar 16 ga Satumba, 2000. Masu bincike suna zarginsa da taka rawar babban mai tsara makircin. Memba ne a rukunin sojan kaki, an nada Kanal Ma’aji a matsayin Laftanar Kanal a shekarar 2013, ya zama cikakken Kanal bayan shekaru hudu. Hafsin mai shekaru 49 shi ne Kwamandan Battalion na 19 na Sojojin Najeriya da ke Okitipupa, jahar Ondo.

Ya halarci Operation Crocodile Smile II,wani atisaye na soja da Sojojin Najeriya suka gudanar a shekarar 2017 don magance matsalolin tsaro a yankin Niger Delta da wasu sassan Kudu-maso-Yamma. Ya kuma yi aiki a Depot, Sojojin Najeriya, daga baya kuma ya zama Kwamandan, Operation Delta Safe. Ya kasance memba na Regular Course 47 na NDA.

3. Laftanar Kanal S. Bappah

   Laftanar Kanal Bappah,memba ne na Nigerian Army Signals Corps, mai lamba N/13036. Dan jahar Bauchi ne a Arewa-maso-Gabashin Najeriya. An haife shi a ranar 21 ga Yuni, 1984. Hafsan mai shekaru 41 ya fara horon cadet a ranar 27 ga Satumba,2004, ya kammala a ranar 4 ga Oktoba, 2008. Memba ne na Regular Course 56 na NDA.

4. Laftanar Kanal A.A. Hayatu

   Laftanar Kanal Hayatu mai lamba N/13038,dan jahar Kaduna ne.

   An haife shi a ranar 13 ga Agusta,1983. Ya yi horon cadet daga ranar 27 ga Satumba, 2004 zuwa 04 ga Oktoba, 2008.

   Memba ne a rukunin sojan kaki,kuma memba ne na Regular Course 56.

5. Laftanar Kanal P. Dangnap

   Laftanar Kanal Dangnap dan jahar Plateau ne.An haife shi a ranar 1 ga Afrilu, 1986. A shekarar 2015, an gurfanar da shi gaban kotun soji tare da wasu mutane 29 saboda laifuffukan da suka shafi yaki da Boko Haram.

   Hafsin mai shekaru 39,mai lamba N/13025, ya fara horon cadet a ranar 27 ga Satumba, 2004, ya kammala a ranar 4 ga Oktoba, 2008.

   Hafsin sojan kaki ne,kuma memba ne na Regular Course 56 na NDA.

6. Laftanar Kanal M. Almakura

   Memba ne na Regular Course 56,Laftanar Kanal Al Makura, dan jahar Nasarawa ne. An haife shi a ranar 18 ga Maris, 1983.

   Hafsin sojan kaki mai lamba N/12983 ya yi horo a matsayin cadet a NDA daga ranar 27 ga Satumba,2004 zuwa 4 ga Oktoba, 2008.

7. Manjo A. J Ibrahim

   Manjo Ibrahim mai lamba N/13065,dan jahar Gombe ne.

   An haife shi a ranar 12 ga Yuni,1987. Hafsin sojan kaki ne wanda ya yi horo daga ranar 27 ga Satumba, 2004 zuwa 4 ga Oktoba, 2008.

   Memba ne na Regular Course 56,kuma ya zama Kyaftin a shekarar 2013.

8. Manjo M.M. Jiddah

   Dan asalin jahar Katsina ne,an haife shi a ranar 9 ga Yuli, 1985.

   Ya yi horo daga ranar 27 ga Satumba,2004 zuwa 4 ga Oktoba, 2008.

   Manja Jiddah hafsin sojan kaki ne kuma memba na Regular Course 56.

   Lambar sabis sa ita ce N/13003.

9. Manjo M.A. Usman

   Manja Usman mai lamba N/15400.

   An haife shi a ranar 1 ga Afrilu,1989. Dan babban birnin tarayya, Abuja ne a tsakiyar Najeriya.

   Memba ne na Regular Course 60,hafsin sojan kaki ne wanda ya yi horon cadet a NDA daga ranar 16 ga Agusta, 2008 zuwa 14 ga Satumba, 2012.

10. Manjo D. Yusuf

   Manja Yusuf mai lamba N/14753,memba ne na Ordnance Corps.

   An haife shi a ranar 26 ga Mayu,1988. A matsayin memba na Regular Course 59, Manja Yusuf ya yi horo a NDA daga ranar 7 ga Yuli, 2007 zuwa 8 ga Satumba, 2012.

   Hafsin dan jahar Gombe ne.

11. Manjo I. Dauda

   Manja Dauda ya shiga soja ta hanyar Direct Short Service Commission.

   An haife shi a ranar 26 ga Nuwamba,1983. Hafsin sojan kaki mai lamba N/13625, ya yi horo daga ranar 5 ga Yuni, 2009 zuwa 27 ga Maris, 2010.

   Manja Dauda,dan asalin jihar Jigawa ne, kuma memba ne na Short Service Commission Course 38.

Har zuwa lokacin da ake buga wannan rahoto, bayanai game da sauran hafsoshi biyar da aka jera a kasa ba su da cikakken bayani. Haka nan ana tsare su saboda zargin shiga cikin makircin juyin mulki. Ga wasu ƙananan bayanai game da su:

12. Kyaftin Ibrahim Bello

   Kyaftin Bello mai lamba N/16266.An haife shi a ranar 28 ga Yuli, 1987. Memba ne na Direct Short Service Commission Course 43.

14. Kyaftin A.A Yusuf

   Kyaftin soja ne mai lamba N/16724.

15. Laftanar S.S Felix

   Laftanar soja mai lamba N/18105.

16. Laftanar Commander D. B. Abdullahi

   Ma'aikacin sojan ruwa ne na Najeriya mai lamba NN/3289.

17. Squadron Leader S. B Adamu

   Shugaman squadron din sojan sama ne mai lamba NAF/3481.

Source: Premium Times

Post a Comment

Previous Post Next Post