Jami’an Majalisar Dinkin Duniya Sun Yi Tir Da Mummunan Kisan Kare Dangi A Sudan Yayin Da Sojojin RSF Ke Ci Gaba Da Mamaye Yankuna

 Jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) sun bayyana mummunan kisan ƙare dangi da ake zargin rundunar Rapid Support Forces (RSF) da aikatawa a yankin Darfur na ƙasar Sudan a matsayin abin firgici da ban takaici.

Rikicin Sudan

Rahotanni sun nuna cewa dubban fararen hula ne aka kashe cikin kwanaki kaɗan, ciki har da mata da yara, yayin da RSF da dakarun gwamnati ke ci gaba da gwabza faɗa domin mamaye wasu muhimman yankuna.

António Guterres, Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya bayyana cewa abin da ke faruwa a Sudan na iya zama laifin yaƙin ƙare dangi (war crimes), kuma ya buƙaci a yi gaggawar tsoma bakin ƙasa da ƙasa don kare rayukan fararen hula.

Haka kuma, wakilin musamman na UN kan harkokin Sudan, ya ce an samu rahotannin da ke nuna mutane na gudu daga garuruwansu, yayin da wasu kuma ke boyewa a cikin dazuzzuka domin tsira daga farmakin dakarun RSF.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga RSF da sojojin gwamnati da su dakatar da fadan tare da bada damar kai taimakon jin kai ga mutanen da ke cikin mawuyacin hali.

Tun watan Afrilu 2023 ne aka fara rikicin Sudan, wanda ya haddasa mutuwar fiye da mutane 10,000 da kuma kauracewar sama da miliyan 8 daga gidajensu.

Post a Comment

Previous Post Next Post