CINIKAYYA TSAKANIN 'YANTA'ADDA DA DILLALAN ZINARI A AREWA MASO YAMMACIN NIJERIYA
A cewar rahoton The Daily Trust, a Arewa-Maso-Yammacin Najeriya, wani mummunan ciniki yana bunƙasa a ɓangaren kasuwancin gwal ɗin da ake haƙowa daga jihar Zamfara don samun bindigogin da ke haifar da ta'addanci a yankin.
“Muna musayar gwal da makamai. Muna ba su gwal ɗin, su kuma su kawo mana bindigogi,” in ji sanannen shugaban ’yan daba Kachalla Mati, a cikin wata taƙaitacciyar hira da aka yi da shi. “Wani lokaci muna sayar da shi a nan; wani lokacin kuma muna aika shi zuwa Dubai.”
Mati, wanda ake kyauta zaton ya gaji Halilu Sububu da aka kashe, yana kula da sansanonin haƙar ma’adinai da dama da ke warwatse a Anka, Kawaye da Ɗan-kamfani a jihar Zamfara. A cewar binciken Daily Trust, yana samun kusan Naira miliyan 200 zuwa ɗari 300 a kowane mako daga haƙar gwal ba bisa ƙa’ida ba.
Ya amsa da cewa, suna amfani da kuɗin da suke samu wajen sayen makamai daga masu sayar da su a kan iyakar Najeriya da Nijar da kuma Mali.
Cinikin yana da sauƙi, amma yana da matukar illa. Gwal ɗin da ake haƙowa, ana haƙo shi ne ta ƙarfin tsaron bindiga. Ana tattara shi, ana shigo da shi ba bisa ƙa’ida ba ta kan iyakoki. Kuma ana musayar shi kai tsaye da masu safarar bindigogi. Waɗannan ’yan kasuwa suna samar mana da bindigogi masu sarrafa kai, harsasai, da babura da ake amfani da su wajen kai hare-hare kan ƙauyuka. Idan ba za a iya yin musayar kai tsaye ba, ana sayar da gwal ɗin a kasuwannin "Black market" da ke yankin, kuma ana amfani da kuɗin da ake samu wajen sayen makamai daga wurin masu shiga yankin Sahel.
A tsawon lokaci, tuni ’yan daba irin su Mati suka rikiɗe suka zama ’yan fashi da kuma yin garkuwa da mutane. Kuma suka haɗa kai da manyan 'yanbindiga waɗanda ke da tsarin haƙar ma’adinai. A yawancin al’ummomi, akan tilasta wa ma’aikatan haƙar ma’adinai yin aiki a ƙarƙashin 'yanta'adda. Waɗanda suka ƙi, ana yi musu azaba ko kuma a kashe su.
“Suna bugun mu, wani lokacin su harbe mu don tsoratar da mu,” in ji wani mai haƙar ma’adinai a Anka. “Muna tona, muna wankawa, su kuma suna kwashe gwal ɗin.”
Don kiyaye doka da kuma guje wa rikice-rikice, mutanen Mati suna ba da “takaddun haƙar ma’adinai” - ƙananan takaddun hatimai masu ɗauke da sunansa. Riƙon wannan takardar yana kare mai riƙonta daga harin wasu ƙungiyoyi. Har ila yau, takaddun suna zama shaida cewa mai haƙar ma’adinai yana ƙarƙashin ikon Mati, kuma dole ne ya miƙa wani ɓangare na gwal ɗin da ya samu a sansanin shugaban.
Ta hanyar waɗannan hanyoyin, ’yan daba sun ƙirƙiri wani tattalin arziƙi na ɓoye wanda ya yi hamayya da na gwal na yau da kullun. “Ba mu amince da bankuna ba” in ji Mati. “Gwal ya fi kyau. Kuɗi ne da za ka iya ɗauka a ko’ina.”
Ana shigo da gwal ɗin daga filayen Mati ba bisa ƙa’ida ba ta Nijar da Mali, inda masu fataucin yankin ke tace "Gold" ɗin, kuma su sake sayar da shi ga dillalan da ke da alaƙa da kasuwar gwal ta Dubai. Wani rahoto na SWISSAID na 2024 ya tabbatar da cewa yawancin gwal ɗin Najeriya da ba a bayyana adadinsa ba yana ƙarewa a cikin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta wannan haramtacciyar hanyar.
A cikin tsarin mulkin ’yan daba, gwal ba wai kawai dukiya ba ne, a'a tsira da mutunci ne. Yana ba da kuɗin sayan babura don kai hare-hare, yana biyan ’yan bindiga, kuma yana tabbatar da ƙawance tare da masu safarar bindigogi daga ƙasashen maƙwabta.
“Muna amfani da gwal ɗin don kare kanmu,” Mati ya yi alfahari. “Idan gwamnati ta kai mana hari, muna kare kanmu. Shi ya sa muke buƙatar bindigogi.”
Amma ga dubban ƙauyukan da ke zaune a ƙarƙashin mulkinsu, wannan “kariyar kai ne” wato na nufin tsaro game da tashin hankali akai-akai. Kuma ga ’yan daba, wadatar gwal da bindigogi ya zama abin - dogaro wanda ke sa dole su ci gaba da yaƙin da suke yi da gwamnati.
