Rahotanni daga turai sun bayyana cewa ƙungiyoyi uku na gasar Premier League suna fafatawa wajen ganin sun samu dan wasan tsakiya Karl Etta Eyong, wanda ke taka leda a nahiyar Turai.
Haka kuma, AC Milan ta nuna sha’awarta ta daukar Joshua Zirkzee daga Bologna a matsayin aron wasa (loan deal), bayan tattaunawar da ta yi da wakilan dan wasan domin karfafa gaban su a kakar wasa mai zuwa.
A gefe guda, rahotanni daga kasar Spain sun nuna cewa Barcelona tana nuna sha’awa wajen daukar dan wasan Najeriya Victor Osimhen, wanda ke taka leda a Napoli.
Kodayake Barcelona na fuskantar matsalolin kudi, kulob din yana nazarin yiwuwar hada wasu ‘yan wasa a cikin yarjejeniya domin rage farashin Osimhen, wanda rahotanni ke cewa farashinsa ya kai sama da €100m.
Masu sharhi na ganin cewa wadannan matakai na iya sauya yanayin kasuwar canja wuri ta wannan kaka, musamman idan Barcelona ta samu nasarar daukar dan wasan Najeriya.