Dino Melaye Ya Caccaki Shugaba Tinubu Kan Yafe Wa Masu Laifin Miyagun Kwayoyi

Tsohon Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Barista Dino Melaye, ya bayyana suka mai tsanani ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan yafiyar da ya bai wa wasu masu laifin miyagun ƙwayoyi da ke tsare a gidajen yari, yana mai cewa wannan mataki ya rusa shekaru da dama na ƙoƙarin Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) wajen yaƙar fataucin ƙwayoyi.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren Lahadi, Melaye ya bayyana cewa matakin da Shugaban Ƙasa ya ɗauka “ba a taɓa ganin irinsa ba” tare da cewa ya yi matuƙar raunana yaƙin da Najeriya ke yi da fataucin miyagun ƙwayoyi.

“Yafiyar da Shugaba Tinubu ya bai wa manyan masu fataucin kwayoyi 70 abin mamaki ne a tarihin duniya. Bincike ya nuna cewa ba a taɓa yin irin haka ba a tarihin kowace ƙasa,” in ji Melaye.

Tsohon ɗan majalisar ya ƙara da cewa wannan shawara ta gwamnatin Tinubu tana aika saƙo mara kyau ga ƙasashen duniya da masu bibiyar yaƙin Najeriya da laifukan ƙwayoyi.

“Shawarata ga Shugaban Ƙasa ita ce ya soke NDLEA, domin matakinsa ya mayar da dukkan ƙoƙarin hukumar tun asali abin ban dariya,” Melaye ya ƙara da cewa.

A tuna cewa a ranar Alhamis, Shugaba Tinubu ya yi amfani da ikon yafiya inda ya bai wa mutane 175 alfarma — ciki har da 82 da aka yafe musu gaba ɗaya, 65 da aka rage musu hukunci, da kuma mutane 7 da ke kan layin kisa da aka mayar da hukuncin su zuwa ɗaurin rai da rai.

Rahoton LEADERSHIP ya nuna cewa kalaman Melaye sun ƙara ƙarfafa jerin suka daga jama’a da ke tambayar dalilin saka masu manyan laifuka — musamman kisa da fataucin miyagun ƙwayoyi — cikin jerin waɗanda aka yi wa afuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post