A ƙasar India, hukumomi sun fara kama wasu matasa Musulmai bisa zargin “tayar da hankalin jama’a” bayan da suka bayyana kalmar “I love Muhammad” a shafukan sada zumunta da kuma a wasu taruka. Wannan lamari ya tayar da kura a ƙasar, inda wasu ke ganin cewa matakin na nuna wariya da tsana ga Musulmi.
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu daga cikin waɗanda aka kama sun bayyana soyayyarsu ga Annabi Muhammad (SAW) ne a matsayin martani ga wasu kalaman ɓatanci da aka yi a dandalin intanet. Sai dai, maimakon a hukunta waɗanda suka yi ɓatancin, hukumomin India sun kama waɗanda suka nuna soyayya da girmamawa ga Annabi.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da dama sun bayyana damuwarsu kan yadda hukumomi ke amfani da dokokin “tsaro” wajen takura wa Musulmi a ƙasar. Sun ce irin waɗannan matakai na iya ƙara rura wutar gaba tsakanin al’ummomi, maimakon taimaka wa zaman lafiya da fahimtar juna a ƙasar da ke da bambance-bambancen addinai.