Gwamnatin Najeriya Ta Cire Darasin Lissafi Daga Cikin Sharuddan Shiga Jami’a

 Matakin ya kawo sabuwar dama ga ɗalibai masu sha’awar karantar fannonin da ba su dogara da lissafi kai tsaye ba.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ɗauki sabon mataki da ya jawo cece-kuce a tsakanin masana da ɗalibai, bayan da ta sanar da cire darasin lissafi daga cikin sharuɗɗan da ake buƙata domin samun gurbin karatu a wasu fannonin ilimi a jami’o’i.

A cewar ma’aikatar ilimi, wannan sauyi ya shafi fannonin da ba su dogara da lissafi kai tsaye ba, kamar arts, humanities, da wasu ɓangarorin zamantakewa, domin a bai wa ɗalibai masu ƙwarewa a waɗannan fannonin damar ci gaba da karatu ba tare da cikas ba. Matakin, in ji gwamnati, yana nufin “ƙarfafa ilimi bisa baiwa da sha’awa, ba tilas da ƙa’idojin da ba dole ba.”

Sai dai, masana ilimi sun bayyana damuwa cewa cire lissafi daga jerin sharuɗɗan na iya rage sha’awar ɗalibai ga fannonin kimiyya da fasaha, waɗanda su ke jagorantar ci gaban zamani. Duk da haka, wasu sun yaba da matakin, suna cewa zai rage matsin lamba ga ɗalibai da ke da ƙalubale wajen lissafi amma ke da hazaƙa a wasu fannoni.

Post a Comment

Previous Post Next Post