Ministan lafiya Farfesa Muhammad Ali Pate, ya ce za a mayar da Asibitin zuwa babbar cibiyar kula da jinya, nazari, horarwa da samar da maganin dafin maciji. A yayin ziyarar tasa, Farfesa Pate ya ƙaddamar da wani sabon sashin bada agajin gaggawa a babban asibitin Kaltungo tare da ƙaddamar da babbar cibiyar kula da lafiya ta Ture Balam.
Ministan ya miƙa wa gwamnatin jihar Gombe tallafin kayan aikin Asibiti da kuma magunguna daga gwamnatin tarayya, inda ya shaida cewar jihar Gombe tavfi kowacce jiha samun kaso mai gwaɓi na wannan tallafi saboda jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da harkar lafiya. A nasa Jawabin gwamna Inuwa Yahaya, ya yaba da haɗin gwiwar da aka yi a ƙarƙashin shirin Renewed Hope, inda ya bayyana haɗakar da ƙarfafa harkar kiwon lafiya.
