Yau shekaru 44 da kashe shugaban ƙasar Masar Anwar Sadat (Egypt) ta hannun masu tsattsauran ra'ayi. An kashe shugaban Masar Anwar Sadat ne a ranar 6 ga Oktoban 1981, ta hannun masu tsattsauran ra'ayin Islama a lokacin da yake duba wani faretin soji a birnin Alkahira. Harin da 'yan ƙungiyar Jihadin Islama ta Masar suka kai, na nuna adawa da yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin Sadat ta ƙulla da Isra'ila. An harbe Sadat ne a lokacin da yake duba fareti a ranar tunawa da sojoji ta shekara-shekara a gundumar Nasr City na Alkahira.
Wasu gungun mahara a ƙarƙashin jagorancin Laftanar Khalid Islambouli, sun tsaya da babbar motarsu a gaban inda Sadat ke zaune tare da manyan baƙi. Maharan sun yi tsalle sun yi harbi da bindigogi masu sarrafa kansu tare da jefa gurneti a kan su Sadat. Baya ga mutuwar Sadat, an kashe wasu mutane goma sha ɗaya, sannan ashirin da takwas sun jikkata a harin, ciki har da mataimakin shugaban ƙasar Hosni Mubarak.
Masu kisan gillar sun kasance masu tsattsauran ra'ayin Islama daga ƙungiyar Jihadin Islama ta Masar. Suna kallon Sadat a matsayin maci amana, saboda alaƙar diflomasiyya da ya ƙulla da Isra'ila da kuma zargin da suke yi masa na yunƙurin murƙushe Islama. Daga baya an kashe jagoran maharan Islambouli da abokan haɗakarsa. Ga masu kishin Islama da yawa, suna ganin masu kisan gillar a matsayin shahidai.
