Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin faɗaɗa tsarin tallafin kuɗi da ake bai wa al’ummar ƙasa mafi rauni domin rage tasirin matsin tattalin arziƙin da ake fuskanta a halin yanzu. Wannan shiri yana nufin kai taimako kai tsaye ga gidajen da suka fi fama da talauci a fadin ƙasar.
Da yake jawabi a taron Oxford Global Think Tank Leadership Conference da aka gudanar a Abuja ranar Talata, Ministan Kuɗi kuma Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziƙin ƙasa, Wale Edun, ya amince da cewa ‘yan Najeriya na fama da hauhawar farashin abinci da na sufuri, amma ya jaddada cewa gwamnati ta ɗauki matakai don rage wannan raɗaɗi.A watan Satumba da ya gabata, ministan ya bayyana cewa gidaje miliyan 8.5 ne suka riga suka karɓi Naira 25,000 kowane gida a ƙarƙashin shirin tallafin kuɗi.
A cewar Edun, kowane gida mai ƙaramin karfi na karɓar N25,000 sau uku. A watan da ya gabata, gwamnati ta bayyana cewa ta kashe kimanin biliyan N330 wajen gudanar da shirye-shiryen tallafin daga watan Janairu zuwa Satumba 2025.
Sai dai adadin waɗanda suka amfana da shirin ya haifar da ce-ce-ku-ce, inda ƙungiyoyin ƙwadago da wasu ‘yan ƙasa ke neman hujjojin sahihin jerin sunayen waɗanda suka karɓi kuɗin.
Gwamnatin ta sanya buri na kaiwa gidaje miliyan 15 a duk fadin ƙasar, wanda har yanzu ake kan aiwatarwa.
Edun ya ce, duk da cewa an samu ci gaba wajen daidaita hauhawar farashi da musayar kuɗi, har yanzu akwai buƙatar ƙarin matakai don fitar da ‘yan ƙasa daga ƙangin talauci.
“Ana ƙoƙarin ganin cewa raɗaɗin sauye-sauyen tattalin arziƙi ba ya da tsanani. Saboda haka aka samar da tsarin biyan kuɗi kai tsaye ga gidaje miliyan 15 cikin gaskiya da tsantseni,” in ji shi.
Ya kara da cewa an samar da tsarin da ke tabbatar da ingantaccen sa ido, gaskiya da bin diddigi kai tsaye a yayin rabon tallafin.
Game da korafin wasu yankuna da ba su karɓi tallafin ba, ministan ya bayyana cewa gwamnati za ta saki bayanan sunayen masu karɓa da suka karɓi kuɗin a kashi na farko, na biyu, da na uku.
Baya ga rabon kuɗin tallafi, Edun ya ce gwamnati ta ƙaddamar da wani shirin ci gaban unguwanni (wards) da zai kai albarkatu, bayanai da kuɗaɗe kai tsaye zuwa unguwa 8,809 da ke cikin ƙananan hukumomi 774 na ƙasar.
“Shirin zai ƙarfafa mutanen da ke aiki a matakin unguwa — musamman ‘yan kasuwa, masana’antu ƙanana da masu sana’o’i — domin ƙara samar da kaya da ƙirƙirar hanyoyin dogaro da kai,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa an tsara gyare-gyaren tattalin arziƙin ne domin tabbatar da daidaito da kuma sauƙaƙa rayuwa ga al’umma.
A nata jawabin, tsohuwar shugabar hukumar SEC, wadda kuma ta kafa Oxford Global Think Tank, Ms Arunma Oteh, ta jaddada buƙatar samar da dogon zuba jari, gina manyan ababen more rayuwa da kuma bai wa jihohi ikon kula da ma’adanan su domin samar da ci gaba mai ɗorewa.
Oteh, wadda ita ce Mataimakiyar Shugabar Bankin Duniya, ta ce Najeriya za ta iya cimma cikakken ƙarfin tattalin arziƙinta ne kawai idan ta samar da yanayi mai jawo zuba jari na dogon lokaci daga gwamnati da masu zaman kansu.
Ta ce babbar matsalar ci gaban ƙasa ita ce rashin isassun ababen more rayuwa, tana mai cewa China na zuba kusan kashi 24% na GDP ɗinta a kan gine-gine, yayin da Najeriya ke kashe tsakanin kashi 4 zuwa 5% kawai.
“Don mu rage giɓin ababen more rayuwa, dole mu ƙara wannan kaso zuwa aƙalla kashi 12% na GDP,” in ji ta.
Ta yaba da wasu matakan da gwamnati ta ɗauka, amma ta buƙaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da Ma’aikatar Kuɗi su ƙara ƙoƙari wajen samar da kuɗaɗen jari mai araha ga ‘yan kasuwa ƙanana da manyan ayyukan gwamnati.
Bugu da ƙari, Oteh ta jaddada buƙatar sauya akalar tattalin arziƙin Najeriya ta hanyar ma’adanan ƙasa, tana mai cewa ƙasar na da aƙalla ma’adinai 40 da za a iya fitarwa amma ba a ci moriyarsu ba.
“Me ya sa ba ma fitar da waɗannan ma’adanai 40 ba? Me ya sa har yanzu suna cikin jerin dokokin gwamnatin tarayya? Ya kamata a bai wa jihohi dama su ci gajiyar albarkatun ƙasarsu,” in ji ta.
Ta kuma bayyana cewa Oxford Global Project na shirin wallafa rahoto na musamman mai taken “Reforming Africa’s Mineral Sector to Prosper Africa” domin nuna muhimmancin albarkatun nahiyar.
Game da jagoranci, Oteh ta ce, “Najeriya na bukatar shugabanni masu hali, tausayi, ƙwarewa da jarumtaka.” Ta bukaci matasa su rungumi waɗannan dabi’u domin ci gaban ƙasa.
“Kakanninmu sun koya mana cewa shugabanci yana nufin yin abin da ya dace, ko da yana da wuya. Idan muka samu irin wannan shugabanci, matasa za su ɗaukaka Najeriya,” ta ce.
A ƙarshe, ta kira haɗin kai tsakanin gwamnati, ‘yan kasuwa da jama’a don zuba jari a ƙasa da ƙirƙirar damar ci gaba ga kowa.
A nasa bangaren, tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya kuma Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ya bayyana cewa matsin tattalin arziƙin da ake ciki yanzu sakamakon jinkirin cire tallafin man fetur ne tun shekaru fiye da goma da suka wuce.
Sanusi ya ce rashin fahimtar ƙa’idodin tattalin arziƙi na asali ne ke sa ‘yan ƙasa su ɗora wa CBN da Ma’aikatar Kuɗi nauyin da bai kamata ba.
Ya bayyana cire tallafin man fetur a matsayin mataki na gyara, ba takura ba.
“Idan kana biya N65 a lita sannan ka fara biyan N160, tabbas za a ji zafi. Amma aikin shugabanci shi ne rage radadin, ba guje wa gyara ba,” in ji shi.
Ya ce tsarin tallafin da aka yi a baya ba tallafi ba ne, illa tattalin “hedge” ne mara iyaka, wanda ya sanya gwamnati cikin asara mai tsanani.
“Gwamnati ta tabbatar wa ‘yan Najeriya miliyan 200 cewa ba za su biya fiye da farashi ɗaya ba, komai sauyin farashin man ko musayar kuɗi. Gwamnati ce ke biyan bambanci — daga $40 zuwa $140, daga N155 zuwa N300. Wannan ba tallafi ba ne, haɗari ne mai zaman kansa,” in ji Sanusi.
Ya ce a ƙarshe, Najeriya ta kai matsayin da take karɓar bashi don biyan tallafi da kuma riba kan bashin, yana kiran hakan “kare tattalin arziƙi da bashi.”
Sanusi ya tuna cewa tun a 2012 ya yi gargadin cewa jinkirin cire tallafin zai janyo babbar wahala daga baya.
“Da an cire shi a wancan lokaci, hauhawar farashi da ta tashi daga 11% zuwa 13% za ta daidaita. Yanzu muna fama da hauhawar farashi sama da 30%. Wannan shi ne sakamakon jinkiri,” in ji shi.
Ya kuma yaba wa sabon Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, bisa jajircewa da ƙwarewa.
“Aikin Babban Banki ba shi ne ƙirƙirar ci gaba kai tsaye ba, amma samar da yanayin da zai ba ci gaba dama. Ina ganin sabon jagorancin yana yin aiki mai kyau,” in ji Sanusi.