Ɗaya daga cikin dalilan da ya sa Majalisar Tsarin Mulkin Kamaru ta ɗauki kwana 15 kafin sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar, shi ne sauraron dukkan ƙorafe-ƙorafen zaɓen - hakan na nufin bayan sanar da sakamakon babu wani abu da mai ƙorafi zai iya yi.
Kan hakan ne BBC ta tuntuɓi masana kimiyyar siyasa guda biyu da suka haɗa da Farfesa Ibrahim Umara, masanan kimiyar siyasa a jami'ar Maiduguri da Farfesa Abubakar Kari na jami'ar Abuja da ke Najeriya.
"Idan ya ce bai yarda ba ma to ai ba za ka daki mutum ka hana shi kuka ba amma kuma ya san cewa ba shi da ƴansanda kuma ba shi da soja. Duk da cewa Bakary da magoya bayansa sun ci buri a wannan karo to amma dole ne su yi haƙuri su tara a gaba."
"Abin da ya sa ya kamata su yi hakuri shi ne Afirka ba za ta jure wani sabon rikicin a Kamaru ba wadda kusan da ma ita kaɗai ce a yankin tafkin Tchadi ke da ɗan zaman lafiya. Jamahuriyar tsakiyar Afirka ba sa zaman lafiya. Haka ma Congo da ƙasar Tchadi da ma Najeriya," in ji Farfesa Ibrahim Umara.
Shi ma Farfesa Abubakar Kari ya ce a halin da ake ciki zaɓin da ya rage wa Issa Tchiroma shi ne ya ɗauki ƙaddara.
"Mafi sauƙin abin da zai yi shi ne ya rungumi ƙaddara amma abin kamar da wuya. Ya yarda a kan cewa an kayar da shi ya jira har zuwa wani lokaci to amma abubuwa da dama sun sauya a Kamarun da ba zai bar hakan ta faru ba," in ji Farfesa Kari.
Farfesa Kari ya kuma ƙara da cewa bisa la'akari da irin karɓuwar da Issa Tchiroma Bakary ya yi a wurin ƴan ƙasar ka iya sa dole ko dai gwamnatin Paul Biya ko kuma ƙasashen duniya su zauna da Bakary a ƙulla wata yarjejeniya.
"Idan masu bore suka ci gaba da bore sannan hakanya ƙara ruruta wutar masu tayar da ƙayar baya a ƙasar, to lallai zama da Bakary domin cimma yarjejeniya zai zama dole. Sai dai kuma abubuwan da za su iya faruwa a nan su ne za su tabbatar da komai. Amma dai ƙasar na kan siraɗi," in ji Farfesa Kari.
