Tsohon Minista Ya Zama Shugaban Gudanarwa Na Jami'a

Tsohon ministan harkokin jiragen sama (Aviation), ya zama shugaban jami'ar Umaru Musa 'yar'adua da ke Katsina.

Gwamnan jihar Katsina Malam Umaru Dikko Raɗɗa Ph.D ya amince da naɗin tsohon ministan Sanata Hadi Sirika wanda ya fito daga shiyyar Daura, a matsayin Shugaban Gudanarwa (Pro Chancellor) na Jami'ar Umaru Musa'Yar'adua da ke Katsina (UMYUK), Wanda zai shafe tsawon shekaru biyar cif daga ranar 24/10/2025 yana riƙe da wannan kujera. 

Sanata Hadi Sirika shi ne aka yi wa naɗin (Marusan Katsina),  ya kuma shafe shekaru takwas tare da marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin minista.
Sakataren gwamnatin jihar Katsina Hon. Abdullahi Garba Faskari ya bayyana cewa, an ba wa Sanata Hadi Sirika wannan aiki ne saboda irin gudummuwar da ya bayar a fannoni daban-daban na aikin gwamnati da ma shugabanci.

Post a Comment

Previous Post Next Post