Gamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Radda ta kafa wani kwamiti na musamman da zai duba yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla tsakanin barayin daji da al’ummomin yankunan da ke fama da matsalolin tsaro a fadin jihar.
An kafa kwamitin ne a ranar Talata, 28 ga watan Oktoba, 2025, karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, wanda ya jagoranci taron kafa kwamitin tare da kaddamar da ayyukansa.
Kwamitin, wanda Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Katsina zai jagoranta, ya ƙunshi wakilai daga muhimman hukumomin tsaro da sassan gwamnati. Ciki har da Kwamishinan Harkokin Tsaro na Cikin Gida na Jihar Katsina wanda zai kasance Sakataren kwamitin, da kuma wakilai daga rundunar Sojoji ta 17 Brigade, da 213 Forward Operation Base (FOB), da hukumar ‘Yan Sanda Farin Kaya, da wakilci daga Babbar Kotun Jihar Katsina, da wasu muhimman hukumomi.
Manufar kafa kwamitin ita ce duba yadda aka gudanar da yarjejeniyar zaman lafiya, da kuma bayar da shawarwari ga gwamnati kan matakan da za su tabbatar da dorewar yarjejeniyar da kuma tabbatar da cikakken zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.
A yayin kaddamar da kwamitin, Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin dabarun Gwamna Radda na tabbatar da tsaro da zaman lafiya mai dorewa a jihar.
Ya ce, “Gwamnatin Katsina ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin cewa an samu zaman lafiya mai dorewa a dukkan yankuna. Wannan kwamiti zai bayar da cikakken rahoto cikin makonni biyu masu zuwa domin samar da sahihan matakai na ci gaba.”
Kwamitin zai fara aikin sa nan take, tare da ziyarar sassan da suka fi fuskantar matsalar tsaro domin tattara bayanai kai tsaye daga al’ummomin da abin ya shafa.
Zuwa yanzu, gwamnatin jihar ta nuna jajircewarta wajen haɗa kai da hukumomin tsaro da shugabannin al’umma don tabbatar da dorewar zaman lafiya a fadin Katsina.
