Rahotanni daga Catalonia sun bayyana cewa ƙungiyar Barcelona ta nuna damuwa da takaici kan wasu maganganu da ɗan wasanta Lamine Yamal ya yi kwanan nan, tare da halayensa a wajen fili.
A cewar rahoton, kulob ɗin ya bayyana cewa furucin da Yamal ya yi ya ƙara wa ‘yan wasan Real Madrid kwarin gwiwa sosai, abin da ake ganin ya taimaka wajen nasarar da suka samu a wasan da aka buga a Bernabeu.
Barcelona ta bayyana cewa wannan kuskure ne na rashin kwarewa da ƙarancin balaga daga matashin ɗan wasan, inda yanzu suka ba wakilinsa Jorge Mendes alhakin kula da harkokinsa, musamman a kafafen sada zumunta da hirarraki da ‘yan jarida.
Kulob ɗin ya kuma bayyana cewa suna son Yamal ya rage bayyana rayuwarsa ta sirri a bainar jama’a, tare da mai da hankali gaba ɗaya kan ci gaban aikinsa a wasan ƙwallon ƙafa.