Halitta Mafi Muni A Duniya Wadda Ake Samu A Karkashin Tekun Australia da Tasmania

 Abun mamaki ba ya ƙarewa a duniya. Da yawan al'umma musamman na Africa, sun san kifaye kala da yawa, amma duk da haka zai yi wahala ka samu wanda ya san Blobfish kasancewar ba a kowane ruwa ake iya samunsa ba. Wannan halitta, tana rayuwa ne a kasan teku, sannan tana da abubuwa da yawa na ban al'ajabi.

Blobfish

MENE NE BOLBFISH?

Blobfish wata halitta ce a cikin teku, yawanci ana samunta a zurfin kusan ƙafa 2,500 daga gaɓar tekun Ostiraliya da Tasmania. Ba a cin ta saboda yawan ruwan da yake jikinta da kuma rashin tsoka. Blobfish ba shi da ƙarfi da tsoka mai ƙarfi, ma'ana ba zai iya yin iyo ko farauta ba. Yana yawo a hankali yana jiran abinci ya shiga bakinsa. An taɓa kiran wannan kifin a matsayin "dabba mafi muni a duniya.

Post a Comment

Previous Post Next Post