Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta fitar da gargaɗin kan ambaliyar ruwa da ta addabi ƙananan hukumomi 20 sakamakon sakin ruwan da ya wuce ƙima daga madatsun Kainji, Shiroro, Zungeru da Jebba.
Ya ja hankalin mazauna bakin koguna da su guji zama a wuraren da ambaliya ke iya kaiwa, su koma wuraren da gwamnati ta tanada a matsayin mafi aminci.
Arah ya bayyana cewa ruwan ambaliya ya lalata gidaje, gonaki, gadoji da hanyoyi a sassa daban-daban na jihar, lamarin da ya naƙasa harkokin yau da kullum.
Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da: Lavun, Magama, Rafi, Kontagora, Gbako, Mokwa, Lapai, Katcha, Agaie, Suleja, Shiroro, Mashegu, Agwara, Bida, Edati, Munya, Bosso, Chanchaga, Paikoro da Wushishi.