Hukumar Kwastan ta Najeriya (NCS) ta fitar da gargaɗi kan wani saƙo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke iƙirarin nuna yawan waɗanda aka tantance daga kowace jiha domin zagayen ƙarshe na ɗaukar ma’aikata a shekarar 2025. A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau, ta ce wannan bayani ba daga gare ta ya fito ba, kuma ba gaskiya bane ba.
A cewar hukumar, tsarin ɗaukar ma’aikata na bana ya fara ne da sanarwar hukuma a ranar 27 ga Disamba, 2024, inda aka samu mutane 573,523 da suka nemi manyan rukunai guda uku da suka haɗa da, Superintendent, Inspectorate da Customs Assistant. Daga ciki, an tantance mutane 286,697 bayan duba takardunsu, sannan aka gayyace su zuwa zagaye na farko na jarabawar kwamfuta (CBT).
Hukumar ta ce daga cikin waɗanda suka shiga wannan jarabawa, masu neman rukunin Superintendent ne kaɗai aka bai wa damar ci gaba zuwa matakin na gaba, wanɗa za a gudanar da shi a cibiyoyi na musamman a kowace shiyya ta kasar nan. Hukumar ta ƙara da cewa wannan tsari ne da zai daidaita manufar adalci, gaskiya, da bin tsarin kowane yanki domin a samu wakilci, tare da tabbatar da cancanta.
NCS ta ja hankalin ‘yan ƙasa musamman masu neman aikin da su dogara da shafukan hukumar domin samun sahihan bayanai, tare da kauce wa yaɗa bayanan ƙarya da ka iya jefa mutane cikin ruɗani ko kuma yaudara.
Hukumar ta kuma tunatar da masu nema cewa duk wani sabon bayani kan ɗaukar ma’aikata ana wallafawa kai tsaye a shafin NCS Recruitment Update Portal ta adireshin https://updates.customs.gov.ng.
