Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) ta gargadi jami’o’i kan jinkirin tura sunayen waɗanda suka amince da su don karɓar shiga makarantu na shekarar 2025, duk da yarjejeniyar da aka cimma a taron manufofin karɓar ɗalibai da aka gudanar tun farkon shekarar.
Hukumar ta bayyana damuwarta cewa, duk da isasshen lokaci da kuma umarnin da aka bayar a fili, har yanzu wasu jami’o’i ba su tura sunayen waɗanda suka amince da su ta hanyar Central Admissions Processing System (CAPS dandamalin hukuma na karɓar ɗalibai zuwa manyan makarantu a Najeriya ba.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja wadda mai magana da yawun JAMB, Dr. Fabian Benjamin, ya sanya wa hannu, hukumar ta ce abin takaici ne cewa wasu jami’o’in gwamnati sun gaza kammala aikin kafin wa’adin watan Satumba, wanda hakan ke karya tsarin da aka amince da shi a taron manufofin.
Sanarwar ta tunatar da jami’o’in cewa, ko da kuwa ba su shirya fara karatun shekara ta ilimi ba tukuna, dole ne su kammala tsarin karɓar ɗalibai kuma su adana bayanan su bisa jadawalin da aka amince da shi.
Saboda haka, JAMB ta umarci waɗannan jami’o’in su fara tsarin karɓar ɗalibai na 2025 nan da nan:
Northwest University, Kano
Nigeria Police Academy, Wudil
Kano State University of Science and Technology, Wudil
Benue State University, Makurdi
Abdulkadir Kure University, Minna
Nigerian Defence Academy, Kaduna
Emmanuel Alayande University of Education, Oyo
Federal University of Medical and Health Sciences, Funtua
Dr. Benjamin ya jaddada cewa duk jami’ar da ta gaza bin jadawalin da aka amince da shi za ta fuskanci matakan ladabtarwa. Ya gargadi cewa dukkan ɗaliban da ba a sarrafa bayanansu ba daga irin waɗannan jami’o’in za a canja musu zuwa wasu makarantu na gaba don yiwuwar karɓa.
A cewar sanarwar:
“Hukumar na kira ga waɗannan jami’o’in da su fara aikin karɓar ɗalibai na shekarar 2025 ba tare da wani jinkiri ba.
Idan suka kasa yin hakan cikin wa’adin da aka kayyade, duk ɗaliban da ba a sarrafa su ba za a tura su kai tsaye zuwa wasu makarantu don yiwuwar karɓa.”
