Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya karyata rahotannin da ke cewa ya danganta marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.
Jonathan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ikechukwu Eze, ya fitar, bayan wasu kafafen labarai sun ba da rahoton da ya karkata daga abin da ya faɗa yayin ƙaddamar da littafin tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor (rtd.).Ya ce rahotannin da ke cewa ya zargi Buhari da hannu a rikicin Boko Haram ba su da tushe.
“A ko da yaushe, Dr. Jonathan bai taɓa cewa ko nuna cewa Buhari na da alaƙa da Boko Haram ko ya taɓa goyon bayansu ba,” in ji sanarwar.
Jonathan ya bayyana cewa kalamansa sun shafi wani lamari da aka ruwaito a baya, inda wasu mutane suka yi ikirarin cewa su ne ke wakiltar Boko Haram, suka kuma am baci manyan ‘yan Najeriya a matsayin masu shiga tsakani — ba tare da saninsu ko yardarsu ba.
Ya ce nufinsa shi ne ya bayyana yadda Boko Haram ke amfani da sunayen mutanen kirki domin tada jijiyoyin wuya da yaudarar jama’a.
Jonathan ya kuma tambayi masu yaɗa irin wannan iƙirari da cewa:
“Idan har Boko Haram sun zaɓi Buhari a matsayin mai shiga tsakani, me ya sa ba su dakatar da ayyukansu na ta’addanci ba lokacin da ya zama shugaban ƙasa?”
Ya tabbatar da cewa shi da Buhari dukkansu sun yi tsayin daka wajen yaki da ta’addanci da mayar da zaman lafiya a Najeriya.Ofishinsa ya roƙi jama’a su yi watsi da duk wani rahoto da aka fassara ba daidai ba, tare da jaddada jajircewarsa wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai, da gaskiya a cikin tattaunawar ƙasa.