An Nada Oluremi Tinubu A Matsayin Sarauniyar Yaki Ta Akko Emirate

 Ƙarramawa ce ga jajircewa da fafutukarra a kan marasa ƙarfi da ɗaliban ‘yan mata

Oluremi Tinubu

Uwargidan Shugaban Najeriya, Senator Oluremi Tinubu, ta samu lambar gargajiya ta Sarauniyar Yaki (Queen Warrior) daga garin Akko, jihar Gombe. Wannan daraja ta zo ne daga Lamido Akko, Alhaji Umar Muhammad Atiku, a lokacin wani bikin karramawa da aka shirya yayin ziyarar aikinta na kwanaki biyu a jihar. 

Lamiɗo ya bayyana cewa an ba ta wannan daraja ne don nuna godiya ga jajircewarta wajen kare marasa ƙarfi da ci gaba da ayyukan jinƙai musamman ga mata da yara a fadin ƙasa. 

A jawabinta, Tinubu ta nuna matuƙar godiya ga wannan yabo tare da ƙara jaddada niyyarta na ci gaba da ƙarfafa ƙoƙarinta wajen inganta rayuwar ɗaliban `yan mata. Ta kuma kira shugabannin gargajiya da su tallafa mata don yaɗa ayyukanta na jinƙai har zuwa matakin ƙauyuka. 

A cikin wannan ziyara, Tinubu ta taya ƙaddamar da shirin Renewed Hope Initiative: Flow With Confidence, wani shiri na ƙasa da nufin bunkasa lafiya da tsaftar al’ada ga `yan mata masu halartar makaranta. 

Post a Comment

Previous Post Next Post