Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, Kotu ta ɗaure mai horaswa shekaru 8 a gidan yari sakamakon lalata da ɗan wasa. Babbar Kotu a Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Musa Dahiru Muhammad, ta yanke wa wani mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa mai suna Hayatu Muhammad hukuncin ɗaurin shekaru takwas a gidan yari ba tare da zaɓin biyan tara ba, bisa laifin aikata luwaɗi da ƙaramin ɗan wasansa.
Wanda aka yanke wa hukuncin, mazaunin unguwar Sanka a cikin birnin Kano, an same shi da aikata laifin sau biyu a wurare daban-daban. Tun da fari, wanda ake tuhuma ya ƙi amincewa da laifin. Sai dai don tabbatar da laifin ba tare da wata shakka ba, lauyan gwamnati na jihar Kano, Barrista Ibrahim Arif Garba, ya kira shaidu biyar waɗanda suka bayar da shaida a gaban kotu.
A gefe guda kuma, wanda ake tuhuma shi kaɗai ne ya tsaya a matsayin shaida a kansa. Laifin ya saɓa da sashe na 284 na Dokar Penal Code. Bayan Mai Shari’a Dahuru ya nazarci bayanan shaidu da kuma hujjojin da aka gabatar a kotu, ya tabbatar da cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin kamar yadda aka tuhume shi. Daga nan sai ya yanke masa hukuncin shekaru huɗu a kowane ɗayan tuhume-tuhume biyu, inda ya umarci a gudanar da hukuncin biyun tare da (concurrently) daga ranar yanke hukuncin.
