Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yi watsi da buƙatar rundunar 'yansandan Najeriya ta a hana zanga-zangar sakin Nnamdi Kanu. A wani rahoto da jaridar The Guardian mai zaman kanta ta ruwaito, ta ce ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya Omoyele Sowore ne ya shirya kuma zai jagoranci zanga-zangar a ranar 20 ga watan Oktoba zuwa kusa da fadar shugaban Najeriya domin buƙatar lallai sai an saki Kanu, wanda ya kwana biyu a ɗaure.
Shugaban ƴansandan Najeriya Kayode Egbetokun ne ya garzaya kotu, inda ya buƙaci babbar kotun ta hana su Sowore gudanar da zanga-zangar.
Sai dai kotun ta ce ba za ta yanke hukunci ba har sai ta ji daga ɗayan ɓangaren, inda ta yi umarni a miƙa takardar ƙarar zuwa ga Sowore, sannan ta ɗage shari'ar zuwa ranar 21 ga watan Oktoba
Sowore ya ce za su yi zanga-zangar ne domin nuna rashin jin daɗinsu kan ci gaba da riƙe da Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar ƙungiyar Ipob, wanda ke tsare tun a shekarar 2021.
