Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana dalilan da ke haddasa matsalar barci ga samari masu tasowa.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa a lokacin da yara maza ke fara balaga, akwai sauye-sauye da dama da ke faruwa a jikinsu, musamman ƙaruwa ko motsi na ƙwayoyin halittar namiji (hormones). Wannan canjin na iya shafar tsarin barci, yana jawo musu matsalar rashin samun isasshen hutu da barci da daddare.
Masana sun ce ƙaruwa ko motsin hormone na testosterone a wannan lokaci na iya sa matasa su zama masu saurin gajiya da rashin nutsuwa, musamman idan ba sa samun daidaitaccen tsarin barci. Hakan na iya shafar karatunsu, yanayin jikinsu, da kuma lafiyar kwakwalwarsu gaba ɗaya.
WHO ta shawarci iyaye da malamai su taimaka wa samari wajen samun kyakkyawan lokaci na barci ta hanyar rage amfani da wayoyi da kallon talabijin kafin kwanciya, tare da tabbatar da cewa matasan suna samun yanayi mai natsuwa da kariya yayin balaga.