Mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya Sanata Kashim Sehtima, zai kai ziyarar aiki jihar Katsina a ranar Talata mai zuwa 21 ga Oktoba, 2025.
Mataimakin shugaban ƙasar zai ziyarci jihar ne domin ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Malam Umaru Dikko Raɗɗa Ph.D ta yi, tare da buɗe taron National MSME Clinic karo Na tara (9).
A ziyarar tasa zai ƙaddamar da sabuwar hanyar zamani da gwamnatin Dikko ta yi wadda ta faro daga babban masallacin Sarki na Juma'a zuwa Shataletalen Kiddies. Har wa yau, zai ƙaddamar da shirin Katsina Sustainable Platform for Agriculture (KASPA).