Gwamnatin Jihar Kebbi ta kulla yarjejeniya da gwamnatin kasar China domin yakar aikata laifuka da ’yan bindiga Lakurawa ke yi a jihar.An cimma yarjejeniyar ne lokacin da Gwamna Nasir Idris ya karɓi tawagar wani kamfani na tsaro na ƙasa da ƙasa, G-Safety, daga ƙasar China, a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Birnin Kebbi. Gwamnan ya bayyana ziyarar kamfanin tsaron a matsayin mai muhimmanci, ganin matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta a wasu kananan hukumomi da ke bakin iyakar Najeriya da Benin da Nijar.
“Muna so ku ba gwamnatin shawara kan muhimman fannoni na tsaro domin mu yi aiki tare da ku da hukumomin tsaro wajen magance matsalolin da wasu kananan hukumomi ke fama da su sakamakon ayyukan ’yan bindigar Lakurawa,” in ji gwamnan.
Da yake magana da manema labarai bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar, mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kamfanin G-Safety, Ahmed Saleh Junior, ya bayyana cewa kamfanin yana da hedkwata a birnin Beijing na ƙasar China, tare da fiye da rassansa 36 a fadin duniya, yana bayar da cikakkun hanyoyin tsaro ga gwamnatoci da cibiyoyi.
Ya tabbatar da cewa wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen ƙarfafa kokarin da ake yi a halin yanzu domin tabbatar da tsaro a jihar da yankin gaba ɗaya daga barazanar ’yan bindiga.