Marc Guehi Ya Ki Sake Rattaba Hannu Da Palace

Ɗan ƙwallon baya na Ingila Marc Guehi, Wanda yake taka leda a ƙungiyar Crystal Palace, ya yi biris da tayin ƙungiyar na tsawaita zamansa a ƙungiyar.
A baya dai ƙungiyar Liverpool na cikin ƙungiyoyin da aka yi zaton za su ɗauke ɗan wasan, domin har gwajin lafiya ya yi domin komawa ƙungiyar da taka leda, amma hakan ba ta faru ba har aka kulle kasuwar cinikin 'yan wasan.
Mai horas da ƙungiyar Palace Oliver Glasner ya bayyana cewa: "Marc ya gaya mana cewa, ba zai sake sa hannu domin tsawaita kwantiraginsa ba. Zai bar ƙungiyar a ƙarshen kakar wasan bana 2026, domin yana son ya jaraba wata ƙungiyar kuma."
Wannan yana nuni da cewa, Marc Guehi zai bar ƙungiyar a matsayin ɗan ƙwallon kyauta.

Wace ƙungiya kuke ganin za ta ɗauke shi?

Post a Comment

Previous Post Next Post