Afghanistan Ta Zargi Pakistan da Karya Yarjejeniyar Zaman Lafiya Bayan Harin Sama da Ya Halaka Mutane 10

 Rikici ya sake ɓarkewa tsakanin ƙasashen maƙwabta bayan kwana biyu da tsagaita wuta.

Pakistan

Gwamnatin Afghanistan ta zargi Pakistan da karya yarjejeniyar tsagaita wuta bayan rahotanni sun tabbatar da cewa harin jiragen saman Pakistan ya kashe aƙalla mutane 10 a yankin da ke iyakar ƙasashen biyu. Harin, wanda ya faru a daren Litinin, ya zo ne kwanaki kaɗan bayan da ƙasashen suka cimma yarjejeniya ta awanni 48 domin dakatar da tashin hankali a kan iyaka.

A cewar jami’an Taliban, jiragen saman Pakistan sun kai hari kan yankunan Khost da Paktika, inda suka lalata gidaje da motocin fararen hula. Hukumomin Pakistan kuwa sun musanta zargin, suna cewa sun mayar da martani ne kan harin da aka kai daga ɓangaren Afghanistan wanda ya kashe sojojinsu.

Masu nazari na ganin wannan sabon rikici na iya sake dagula dangantakar ƙasashen biyu, musamman bayan watanni da dama na zargin juna game da tsaro da kuma rawar da ‘yan ƙungiyar Tehrik-i-Taliban Pakistan (TTP) ke takawa a yankin.

Post a Comment

Previous Post Next Post