Tun lokacin da muna Soyayya Da saurayina, wallahi ban taɓa ganin ya ci abinci ba, ko gidanmu ya zo, idan aka ba shi abinci ba ya ci. Na yi zaton ko tsabar kunya ce, a haka har muka yi aure. Idan na dafa abinci na kawo don mu ci tare ba ya ci. Idan na koma ina kallonsa ma sai ya ƙi ci. Kullum sai ya yi ta kawo man wasu 'yan dalilai da ba su taka kara sun karya ba. Har dai na fara damuwa. Wani abu da ya fi ɗaure man kai shi ne, 'yar aiki ko almajirin gida ba su taɓa wata ɗaya a gidana ba kawai sai in ga sun bar zuwa. Idan na tambaye shi sai ya ce man wai kuɗin da ake ba su ne suka raina, saboda haka za a nemo wani. Kai! ni dai har na fara jin tsoronsa, saboda abubuwan da yake yi don sun jefa ni cikin zargi.
Wata rana ina kwance tsakar dare sai na dinga jin wani ƙugi da ƙara. Sai na gane wannan ba kukan mutum ba ne, kuma ko a dabbobi ban taɓa jin irin wannan kuka ba.
Sai na juyo domin in tashe shi daga bacci domin ya ji halin da ake ciki. Kawai sai ban gan shi ba. Na tashi zaune, na laɓaɓa ina dubawa ɗaki bayan ɗaki. Kwatsam sai na yi arba da shi a falo, kamaninsa duk sun canza. Idanuwansa sun yi tulu-tulu, kuma sun yi jajur. Ya yi face-face cikin jini. Yana ta fizgar ɗanyen nama, daga ganin rigar wanda ke ƙasa kwance, na gane ta almajirin gidan nan ce. Ashe duk shi ke kashe su, yana cinyewa. Yana ta gumji, ya juyo ya kalle ni da idanunsa jajur. Na ɗimauce na fasa ƙara......
