Matatar Dangote ta ce hauhawar farashi da rashin tabbas a farashin ɗanyen mai ne suka sa matatar ta rage sayen ɗanyen man, wanda hakan ya rage fetur da take fitarwa, ba wai saboda matsala daga matatar ba, sannan ta ƙara da cewa ma'aikatan da kamfanin ya sallama sun yi yunƙurin yi musu ɓarna. Kamfanin ya bayyana haka ne a lokacin da mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote Edwin Devakumar yake zagayawa da 'yanjarida cikin matatar bayan rahotanni sun ce matatar ta rage aiki.
"Babu kamfanin da yake aiki ɗari bisa ɗari a kullum ba tare da fuskantar wata matsala ba, abin da ya fi muhimmanci shi ne lura da matsalar da ta shafi abin da ake fitarwa."
Ya ce a tsarin matatar wadda aka buɗe a farkon wannan shekarar, an tsara za a riƙa ɗan dakatawa ne a yi gyare-gyare a duk bayan shekara biyar, ba kamar sauran tsofaffin matatu ba da suke yawan tsayawa da aiki domin gyara."
Sai dai kafar Reuters ta ruwaito matatar ta dakata da aiki domin gyara sau huɗu a wannan shekara, wanda ba kasafai ake ganin haka ba a sababbin matatun mai irin na Dangote.
A game da sallamar ma'aikata na kwanakin baya, Devakumar ya ce sun gano yunƙurin aikata ɓarna har sau 22 da ma'aikatansu suka yi, ciki har da yunƙurin cinna wuta da lalata wasu kayan aiki. Mun san ranar da aka yi da ma duk ɓangaren da aka yi yunƙurin, in ji shi.
