Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Kira Ga Majalisar Malaman Zamfara Da Su Yi Addu’ar Samun Zaman Lafiya

Gwamna Dauda Lawal ya yi kira ga mambobin Majalisar Malaman Zamfara (Zamfara Ulama Council Forum) da su ƙara yin addu’o’i don samun zaman lafiya mai ɗorewa a fadin jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an bayyana cewa gwamnan ya yi wannan kira ne bayan ganawa da Majalisar Malamai ƙarƙashin jagorancin Sheikh Umar Kanoma a Fadar Gwamnati da ke Gusau a ranar Alhamis.

Gwamna Lawal ya jaddada muhimmancin rawar da shugabannin addini ke takawa wajen tsara ra’ayoyin jama’a da kuma inganta zaman lafiya, yana mai lura da cewa malamai suna kusa da mutane kuma suna da amincewar su.

“Shugabannin addini suna taka muhimmiyar rawa a duk abin da muke yi a Zamfara saboda suna kusa da jama’a, kuma al’umma tana sauraron su musamman wajen tsara tunanin jama’a,” in ji shi.

Ya bayyana cewa an samu ci gaba a yaki da ’yan bindiga, amma ya nuna cewa har yanzu akwai bukatar ƙarin ƙoƙari domin cimma cikakkiyar zaman lafiya. Lawal ya kuma bukaci haɗin kai tsakanin gwamnati, shugabannin addini da ’yan kasa domin tabbatar da tsaron jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post