SAURA KWANAKI 3 A RUFE
GASAR RANAR MARUBUTA HAUSA 2025 – SABON SHAFI GA MARUBUTA
Gasar Taron Ranar Marubuta Hausa 2025 ta bambanta da duk wata gasa da aka taɓa gudanarwa a baya. Wannan ba kawai gasa ce ta rubutu ko ƙirƙira ba, hanya ce zuwa duniyar ilimi da fasaha da ci gaba!
Abubuwan da za a samu daga gasar:
1. Horarwa a Fannin Ƙirƙirarriyar Basira (Artificial Intelligence) Za a ba wa waɗanda suka samu nasara damar samun guraben horo na musamman a manyan cibiyoyin AI na duniya, inda za su koyi yadda ake amfani da AI wajen bunƙasa rubutu da fassara, da adabin Hausa.
2. Damar Samun Ayyukan yi: Gasar za ta buɗe ƙofofin samun aiki da haɗin gwiwa da cibiyoyi da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa masu amfani da AI da ilimin harshe.
3. Halartar Taron Ƙasa da Ƙasa: Waɗanda suka fi ƙwarewa za su samu gayyata zuwa tarurruka a manyan jami’o’i da cibiyoyi a ƙasashen waje domin gabatar da aikinsu da samun horo na ƙwarewa.
4. Lambar Yabo da Kyaututtuka: Za a bai wa waɗanda suka lashe gasar lambobin yabo da manhajojin aiki na zamani, da samar masu da gurabun neman tallafin gudanar da ayyukan fasaha ko bincike.
Wannan gasar za ta nuna yadda fasahar Artificial Intelligence (AI) ke iya sauya tunanin marubuta da malamai da masu fassara daga rubutu na gargajiya zuwa fasahar zamani. Gasar za ta ba marubutan Hausa damar:
1. Koyon yadda ake haɗa fasaha da harshe wajen ƙirƙirar labarai.
3. Samun damar yaɗa rubutunsu ga duniya baki ɗaya ta hanyar AI platforms.
3. Faɗakarwa da bunƙasa harshen Hausa ta hanyar ƙirƙira mai inganci da fasaha.