Dubban Mutane Sun Gudanar Da Zanga-Zangar “Babu Sarakuna” A Faɗin Amurka

 Masu zanga-zangar na nuna adawa da manufofin Donald Trump da nufin kare dimokuraɗiyya.

Dubban mutane sun fito kan tituna a manyan biranen Amurka domin gudanar da zanga-zangar da ake kira “No Kings” (wato Babu Sarakuna), domin nuna adawa da abin da suke kira yunƙurin shugaban ƙasa Donald Trump na neman ƙara ƙarfi da iko a siyasar ƙasar.

Masu zanga-zangar sun taru a Washington DC, New York, California, da sauran jihohi, suna ɗauke da kwalaye da rubuce-rubucen da ke kira da a kiyaye tsarin dimokuraɗiyya. Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ce, manufarsu ita ce tunatar da Amurkawa cewa shugabanci ba sarauta ba ne, kuma babu wanda ya fi doka ƙarfi.

Jami’an tsaro sun ce an gudanar da zanga-zangar cikin lumana, ba tare da tashin hankali ba, duk da cewa akwai matakan tsaro da aka ƙara a wasu wurare don tabbatar da zaman lafiya.

Post a Comment

Previous Post Next Post