Yan Sanda Sun Kaddamar Da Bincike Kan Gawar Wata Mata Da Aka Samu Kusa Da Jami’ar Tarayya Gashua

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Yobe ta fara bincike kan mutuwar wata mata mai shekara 45 da aka samu gawarta a kusa da Jami’ar Tarayya Gashua, da ke ƙaramar hukumar Bade a jihar.

Mai magana da yawun rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar. Ya ce wacce ta rasu an gano ta da suna Falmata Abubakar, mazauniyar Abasha, Unguwar Sarkin Hausawa, Gashua, wacce aka samu sanye da hijabi baƙi.

A cewar Abdulkarim, rundunar ta samu rahoto daga wani Yusuf Sarkin Baka, mazaunin Sabon Daula, Bade, game da gano gawar wata mata a kusa da katangar jami’ar.

“Lokacin da  muka samu rahoton, jami’an ‘yan sanda daga sashen Gashua sun garzaya wurin domin gudanar da bincike kai tsaye,” in ji sanarwar.

Rundunar ta ce an ɗauki gawar zuwa Asibitin ƙwararru ta Gashua, inda likita ya tabbatar da mutuwar mamaciyar. Daga nan kuma aka miƙa gawar ga iyalanta bayan kammala binciken likita domin gudanar da jana’iza bisa tsarin Musulunci.

Sai dai binciken farko ya nuna cewa an kawo gawar ne cikin mota, sannan aka yar da ita a wajen da aka samu ta, kimanin kilomita biyu daga gidanta.

Abdulkarim ya ce, “wannan sabon bayani ya karfafa binciken da rundunar ke yi domin gano da kama waɗanda suka aikata wannan ta’asa.”

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, CP Emmanuel Ado, ya tabbatar wa jama’a cewa za a gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin da kuma tabbatar da cewa masu hannu a ciki sun fuskanci hukunci.

Rundunar ta buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da bada haɗin kai ga jami’an tsaro. Haka kuma ta roƙi duk wanda ke da wata masaniya da ta shafi lamarin da ya kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko ta layukan gaggawa na rundunar.

A ƙarshe, rundunar ta jaddada ƙudurinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin Jihar Yobe.

Post a Comment

Previous Post Next Post