Tsibirin Migingo (Migingo Island), wani ɗan ƙaramin tsibirin dutse ne a tafkin Victoria wanda aka daɗe ana taƙaddamar mallakar sa a tsakanin ƙasashen Kenya da Uganda. Kodayake yankin yana cikin ruwan Kenya. Ruwan mai wadatar kifi, cibiyar tattalin arziki ce mai kima, mai jan hankalin masunta wanda kuma ya haifar da rikicin mallaka.
Rikicin tsibirin da ke da faɗin murabba'in mita 2,000 (ƙasa da rabin girman filin wasan ƙwallon kafa) ya fara ne a shekara ta 2004, lokacin da sojojin Uganda suka kafa sansani a tsibirin. Yayin da ake ganin tsibirin da kansa ya na cikin ƙasar Kenya a bisa kan iyakokin da Turawan mulkin mallaka suka shata. Uganda ta tabbatar da cewa wuraren kamun kifi na kogin mafi daraja suna cikin yankin tafkinta. Uganda ta girke 'yan sanda da sojoji a tsibirin na tsawon shekaru, kuma ta kama masuntan ƙasar Kenya. Bayan da farko ta tura nata 'dakarun, Kenya ta janye sojojinta a shekara ta 2007 domin gudun tada zaune tsaye.
Yayin da wasu jami'an Uganda suka amince da kasancewar tsibirin a Kenya, sojojin Uganda na ci gaba da sintiri tare da aiwatar da dokar kamun kifi a cikin ruwan da ke kewaye.
An kiyasta yawan mutanen tsibirin Migingo a cikin 2024 ya kai kusan mutane 500, kodayake wasu majiyoyi sun nuna zai iya kusantar 1,800. Tsibirin yana da cunkoson jama'a sosai saboda ƙankantarsa.
Duk da tattaunawar diflomasiya da binciken haɗin gwiwa a shekarar 2019, ana ci gaba da taƙaddama kan ikon tsibirin. A yanzu Tsibirin yana aiki a zaman ƙauye mai cin gashin kansa, kodayake akwai cunkoson jama'a a wurin. Mazauna ciki har da 'yan Kenya da Uganda, suna zaune kafaɗa-da-kafaɗa a cikin rumfunan da suka cika maƙil.
Tsibirin yana da ofishin 'yan sanda, mashaya da yawa da otal-otal, wuraren shakatawa, da sauran ƙananan kasuwanni. Jami'ai daga Kenya da Uganda ne ke gudanar da ofishin 'yansanda da ke tsibirin. Abubuwan more rayuwa na yau da kullun ba su da kyau a tsibirin, sannan akwai ƙalubalen da suka shafi tsafta, da ruwan sha mai kyau.
