Koyi Yadda Ake Noman Citta Cikin Sauki A Cikin Gida

 Ganin yadda chitta take tsada, ake Kuma buƙatar ta, sannan take da sauƙin raino, yakamata kowa ya iya rainon ta. Indai kana da filin da za ka iya aje buhun siminti, musamman ma yana kusa da inuwa, sannan kana da naira 500, kana kuma da hanyar samun bokitin ruwa ɗaya a kowane sati, to kai ma kana iya fara rainon citta. Abin na da sauƙi sosai. Ga yadda Abin yake:

Citta

1- Da naira 500 ɗinka za ka samu ɗanyar chitta ( ko ƙwara ɗaya aka ba ka ta ishe ka ka fara). Kawai ka tabbatar da ba a yanka cittar ba, sannan tana da aƙalla idanu biyu. 

2- Ka samu ɗan muzubin ruwa  mai faɗin baki kamar "plate" ɗin roba, sai ka zuba ruwa yadda idan ka tsoma cittar, kuma ka kwance, ruwan ba zai shanye cittar ba. 

3- Sai ka aje chittar a cikin ruwan. Kawai ka tabbatar da cittar na kwance ne cikin ruwan, sannan ruwan bai shanye ta ba, musamman gefen da idanun suke. Kada ka Bari ruwan ya shanye idanun. Saboda gudun rubewa. 

4- Sai ka ɓoye mazubin da cittar ke ciki a wani waje mai ɗan duhu, sannan da sanyi. Ya zamanto dai-dai gwargwado akwai iska. 

Kawai ba a son iska da rana su yi yawa saboda kada chiittar ta bushe. Sannan ana son guri mai sanyi da duhu ne saboda chittar ta ji sauƙin tsira. 

5- Za ka riƙa yayyafa ko fesa ma cittar ruwa duk kamar bayan kwana biyu. Amma dai ka lura kada ruwan da ke ƙasanta ya yi yawan da zai shanye ta har ta ruɓe. Idan ma ka ga ruwan ya taru, sai ka rage. 

6- Za ka bar cittarka a wannan yanayi kana yayyafa mata ruwa har wajen sati biyu. 

7- Zuwa kamar sati biyu, cittar ka za ta yi tsiro dai-dai inda waɗannan idanun nata suke. 

8- Idan cittar taka ƙarama ce mai ido ɗaya ko biyu, to kana iya shuka wadda ta fara tsiro. Amma idan tana da ɗan girma, tana kuma da idanun da suka kai uku ko fiye da haka. To ka bar waɗannan tsirran har su ƙara girma. Yadda idan ka zo shuka ta za ka yanka chittar, ka fitar da kowane ido ka shuka shi daban. 

9- Daga nan sai shuka. Ka samu fatar buhun siminti ka zuba ƙasa kamar ɗaya bisa uku na buhun. Yana da kyau ka samu ƙasa mai taki (manure). Amma idan takin kaji ko ko na dabbobi ne za ka gauraya da ƙasar, to ka yi hakan da wuri kafin lokacin da za ka shuka cittar, saboda gudun tsutsa da zafin taki. Sai ka riƙa ba ƙasar ruwa kamar sati ɗaya kafin ka shuka cittar ka. 

10- Da chittarka ta isa shuka, sai ka shuka cikin buhun ƙasar da kake ma ban ruwa. Kawai ka tabbatar da tsiron na kallon sama sannan ba ka danne shi da ƙasa ba. Za ka iya lulluɓe tsiron cittar da ka shuka da, sannan ka tabbatar da ba cikin rana shukar take ba saboda kada zafi ya kashe tsiron.

11- Haka za ka c igaba da ba chittar ruwa kaɗan-kaɗan har tsiron ya girma ya bayyana. Za ka ga ta yi tsawwan haki. Sai ka ci gaba da ba ta ruwa sannu-sannu.

12- Idan ta yi kamar wata ɗaya zuwa biyu, za ka ga chittar ta ƙara tsiro da wasu hakkin, to idan ka so kana iya yanke waɗannan sabbin kunnuwan, ka sake shuka su a wani buhun daban.

13- Za ka ci gaba da ban ruwa aƙalla duk bayan kwana ɗaya, har wajen wata 3-4. 

14- A Hanakali za ka ga cittarka na ta ƙara ganye, wannan ke nuna maka tana ƙara girma. 

15- Za ka bar cittar a ƙasa, kana ban ruwa (idan ba a ruwa) har tsawon wata 3-4. Lokacin za ka ga ganyen ya yi duhu, kawai sai ka tuge chittar ka ga Ikon Allah.

Post a Comment

Previous Post Next Post