Wata kotun majistare da ke Kuje, Abuja, ta bayar da beli ga mai wallafa jarida kuma ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore; ɗaya daga cikin lauyoyin da ke kare shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu — Aloy Ejimakor; ɗan uwan Kanu, Prince Emmanuel Kanu; da wasu mutum goma, kan kuɗin Naira dubu ɗari biyar (₦500,000) kowannensu tare da masu tabbatarwa biyu.
Rahoton PUNCH Online ya ce an cafke waɗannan mutane goma sha uku ne tare da gurfanar da su a gaban kotu bisa zargin tayar da hankalin jama’a da karya doka yayin zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow da aka gudanar a ranar Litinin, 20 ga Oktoba, a Abuja.Ana cewa Ejimakor, Emmanuel da sauran mutum goma sun shiga hannun jami’an tsaro ne yayin zanga-zangar, inda daga baya aka tura su gidan gyaran hali na Kuje. Sowore kuwa, an kama shi ne a ranar 23 ga Oktoba a harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja, bayan ya halarci shari’ar ta’addancin da ake yi wa Kanu domin nuna goyon baya.