Mutane Akalla 25 Sun Rasu a Indiya Bayan Wata Motar Bas Ta Kama Da Wuta.

  Aƙalla mutane 25 ne suka mutu a ƙasar Indiya bayan wata motar bas ta kama wuta sakamakon hatsari da ta yi da babur a yankin Nashik, jihar Maharashtra, a safiyar ranar Lahadi.

Haɗari

Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya faru ne lokacin da babur ɗin ya buga jikin bas ɗin, wanda hakan ya jawo ta kama da wuta cikin gaggawa. Mutane da dama daga cikin fasinjojin da ke cikin motar sun makale a ciki saboda ƙonawar ta da sauri.

Jami’an tsaron ƙasa da na kashe gobara sun isa wurin don ceto mutanen, inda suka samu nasarar ceto mutane 8 da suka ji rauni, amma mutane 25 sun mutu nan take kafin a iya kai musu dauki.

Wani jami’in ‘yan sanda ya shaida wa manema labarai cewa: “Bas ɗin tana ɗauke da fasinjoji daga Surat zuwa Pune lokacin da babur ɗin ya shiga gabanta. Gobarar ta bazu cikin ƴan daƙiƙu saboda mai.”

Shugaban ƙasar Indiya Droupadi Murmu da Firayim Minista Narendra Modi sun mika ta’aziyyarsu ga iyalan waɗanda suka rasa rayuka, tare da bayar da umarni ga hukumomi da su gudanar da cikakken bincike kan dalilin ainihin haɗarin.

Hukumomi sun ce za a biya iyalan mamatan da diyya, kuma gwamnati za ta duba yadda za a ƙara matakan tsaro a hanyoyin motoci don rage irin waɗannan haɗurra a nan gaba.

Post a Comment

Previous Post Next Post